wasu malaman islamiyyu sun sauke Ganduje daga matsayin khadimul islam

Wasu manyan malaman islamiyya a jahar kano sun sauke gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje daga matsayin khadimul islama Idan baku manta ba tun bayan bullar cutar nan ta coronovirus gwamnatin kano ta dauki matakin garkame makarantun boko da Allo dama islamiyyu da kuma gidajen kwallon kafa dama gidajen da ake gudanar da bukukuwa da kuma kasuwannin jahar kano da nufun kare kai daga wannan annamimiyar cuta, Amma bayan daukar wasu tsawan lokuta ahankali ahankali zaa iya cewar anbude gurare dayawa amma banda makarantun islamiyyu dana boko amma kuma a baya bayannan anbude wasu makarantun bokon da nufun wasu dalibai suje su zana jarabawar WAEC da NECO, Kusan zaa iya cewa wannan daliline yasa wasu malaman islamiyyu bude makarantun su amma sai gashi ana bunsu ana kamawa, Wasu malaman islamiyyu dake tarauni sun bayyana cewa yakamata gwamna Ganduje ya duba wannan Al’amari duba da yanda ake masa lakabi da khadimul islama ya wai wayi makarantun islamiyyu domin suna cikin wani hali, Da muka tattauna da wani malamun islmaiyya wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace daga yau sun sauke Gwamna Ganduje daga matsayin khadimul islama domin har yanzu yakiyin wani hobbasa domin bude wadannan makarantu, Kamar yanda kuka sani de anbude gidan kwallon kafa da gidajen bukukuwa amma kuma haryanzu islamiyyu sun gagata budewa   HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

shin kunsan dinbun masoyan da suka tarbi tsohon sarki sunusi a Kaduna?

Tsohon sarki sunusi ya samu tarbar masoya masu dunbun yawa a ciki da wajan jahar Kaduna Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ziyarci gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai. Wannan ce dai ziyara ta farko da sarkin ya kai wata jiha ta Najeriya tun bayan da ya tare a Legas bayan cire shi daga sarauta a watan Maris. A wani saƙo da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce Sarki Sanusi ya yi alƙwarin yin iya bakin ƙoƙarinsa a matsayinsa na shugaban Jami’ar Kaduna, da kuma mataimakin shugaban hukumar bunƙasa zuba jari ta jihar. Kwanaki kaɗan ne bayan cire sarkin daga sarauta gwamna El-Rufai ya ba Sarkin waɗannan muƙaman   HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Afakallahu zai dauki matakin dakatar da saka film me Dogon zango a jahar kano

Shugaban Hukumar tace fina finai a jahar kano Ismail na Abba Afakallahu zai dauki matakin saka film me Dogon zango a jahar kano, Kamar yadda kuka sani dai zaa iya cewa harkokin film din hausa ayanzu kusan kaso sittin acikin dari zamu iya cewa sun koma kan YouTube kuma yawancin masu saka film a YouTube suna sakashi ne ba tare da Hukumar tace fina finai sun taceshi ba, Kuma yawancin yan downloading suna kwafar wannan film a YouTube su dinga siyarwa da mutane batare da sun siya ba Kusan hakanne yasaka wannan Hukumar daukar wannan mataki amma wasu dayawa daga cikin masu shirya wadannan fina finai sun amunce da wannan mataki na wannan hukuma, A tattaunawar da mukai da shugaban kungiyar masu YouTube na arewa Ali Bet kuma shugaban kamfanin brothers tv entertainment ya bayyana mana cewar Munji dadin wannan mataki da wannan hukuma zata dauka sakamakon mutane suna futa su kashe kudinsu suyi wadannan fina finai kudadensu basa dawowa kawai de sunayine domin su ruke tasharsu amma sai ake samun wasu daga cikin masu downloading suna kwafar wannan film suna sayarwa da mutane batare da sun saya ba amma idan wannan hukuma tashigo to zaa samu wani tsari wanda masu shirya fina finai masu Dogon zango zasu dunga samun kudin shiga Ali bet ya bayyana mana cewa ayanzu kanfaninsa yana shirye shiryen daukan wani film me Dogon zango mai suna MIJI DA MATA wanda yace idan har wannan hukuma ta dauki wannan mataki to hakan zai dinga basu damar kawo fina finai masu kayatarwa A yanzu de zamu iya cewa ana daf da cimma matsaya tsakanin Hukumar tace fina finai da kuma masu YouTube a jahar kano HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading