Manchester City za ta dauko Grealish, Sannan Kuma Chelsea na zawarcin Gomes

Manchester City za ta dauko Grealish, Sannan Kuma Chelsea na zawarcin Gomes sannan kuma Manchester city zata duba yiwuwar dauko Jack grealish. Manchester City za ta duba yiwuwar dauko dan wasan Aston Villa Jack Grealish, mai shekara 24, idan Bayern Munich ta sayi dan wasan Jamus Leroy Sane, mai shekara 24. An ce ita ma Manchester United tana zawarcin dan wasan na Ingila. (Telegraph) A shirye Chelsea take ta dauko dan wasan Manchester United Angel Gomes. Kungiyoyin kasashen waje da dama suna zawarcin dan wasan na Ingila dan shekara 19. (Independent) Kazalika Manchester United tana son dauko Grealish domin maye gurbin Gomes. (Express) Newcastle da Arsenal suna cikin kungiyoyin Gasar Firimiya da ke son sayo dan wasan Wolfsburg dan kasar Netherlands Wout Weghorst, mai shekara 27, a kan euro 35m. (Bild – in German) Southampton na sha’awar sayen dan wasan tsakiyar Arsenal Folarin Balogun, dan shekara 18. (Mail) Haka kuma Southampton tana duba yiwuwar dauko dan wasan gaban Faransa Thomas Robert daga Montpellier. Matashin dan wasan mai shekara 19, da ne ga tsohon dan wasan Newcastle Laurent Robert. (Mail) Chelsea ta amince golan Kamaru Andre Onan, mai shekara 24, da dan wasan bayan Argentina Nicolas Tagliafico, mai shekara 27 su koma Ajax. (Sun) kamar yanda BBC ta ruwaito. Dan wasan da ke tsaron bayan Paris St-Germain Layvin Kurzawa ya sabunta kwangilar shekara hudu a kungiyar. An yi ta rade-radin cewa dan wasan na Faransa, mai shekara 27, zai koma Arsenal ko Liverpool. (Goal) Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce kungiyar wacce ta lashe Kofin Firimiya na bana ba za ta kashe “miliyoyin kudi” a kasuwar musayar ‘yan kwallon kafa. (Mirror) ‘Yan wasan Barcelona da dama suna zaman-tsama da kocin kungiyar Quique Setien. (ESPN) Dan wasan Leicester City Dennis Gyamfi, dan shekara 18, zai bar kungiyar idan kwangilarsa ta kare yau, 30 ga watan Yuni. Matashin dan wasan na Netherlands ya ki amsa tayi da dama da kungiyar ta yi masa na sanya hannu kan kwangila. (Leicester Mercury) Zaku iya ci gaba da kasancewa damu a wannan fage na wasanni tare da ni Aminu Asarab HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

‘yan sanda zasu biya ‘yan shi’a kimanin miliyan 15 a matsayin diyya

‘yan sanda zasu biya ‘yan shi’a kimanin miliyan 15 a matsayin diyya bayan zargin da sukai na an kashe musu mutane 3 kuma an hanasu gawar waki. Wata babbar kotun tarayya a Abuja, ta umarci ‘yan sandan Najeriya su biya ‘yan kungiyar Shi’a mabiya Shaikh Ibrahim Elzakzaky Naira miliyan 15 saboda kisan ‘ya’yan kungiyar uku yayin wata zanga-zanga a Abuja. Kotun wacce ta yi zamanta a Abuja babban birnin kasar ta kuma umarci babban asibitin kasa ya bayar da gawarwakin uku nan take domin yi musu jana’iza. A ranar 22 ga watan Yulin 2019 ne aka kashe wasu mabiya kungiyar ta Shi’a yayin wata zanga-zanga da ta rikide zuwa tarzoma. Alokacin zanga-zangar su ma ‘yan sanda sun yi zargin cewa ‘yan Shi’a sun kashe dan sanda, zargin da kungiyar ta IMN ta musanta. Lauyan kungiyar ta IMN Bala Isa Daku ya ce sun garzaya kotun ne bayan hukumomi sun ki ba da gawawwakin domin yi musu jana’iza Kamar yanda Addini ya tanadar. A hukuncin kotun karkashin mai shari’a Taiwo Taiwo, ya ce ‘yan sanda za su biya Naira miliyan ga kowanne mamaci a matsayin diyyar kisan da aka yi. Sai dai kotun ta yi watsi da bukatar cewa a tilasta wa ‘yan sanda su nemi afuwar kisan. Kamar yanda kuka sani de har yanzu shugaban kungiyar yan uwa musulmi ta shi’a wato sheikh Ibrahim El zakzaky de yana hann. Kusan zaa iya cewa ruke wannan babban malami shine dalilin dayasa mabiyansa ke yawan yin zanga zangar.   HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Yanda wakar jarumar mata ta samu wani babban matsayi a Jami’ar Bayero ta kano

LWaƙar Jarumar Mata da ta ja hankali a arewacin Najeriya yanzu kuma ta samu shiga fagen nazari a Jami’a, inda mashahurin malamin nazarin adabin baka Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya feɗe waƙar. Kwarjini da karɓuwa da kuma daɗin waƙar da salonta ake ganin ya ja hankalin masoya musamman matan aure da aka gani a bidiyo suna rausawa a gaban mazajensu, a daidai lokacin da ake cikin yanayin zaman gida na kullen annobar korona. Ana nazarin waƙa ne a fagen ilimi idan ta dace da nazari da kuma abubuwan da nazari yake nema, ƙila wannan ne dalilin da ya ja hankalin Farfesa Gusau mashahurin malamin waƙoƙin baka a Jami’ar Bayero da ke Kano. Farfesan ya feɗe waƙar ne a wata takardar nazari da ya aiko wa BBC mai taken “Feɗe waƙar Jarumar mata ta mawaki Hamisu Yusuf Breaker bisa gadon nazarin waƙar baka Bahaushiya.” Hamisu Breaker ya saki waƙar Jarumar Mata ne dab da bikin Sallah ƙarama, kuma sai ga shi ta samu ƙarɓuwa nan da nan inda wasu matan aure suka ci bikin na sallah da waƙar tare da ɗebe kewar zaman gida. A wata hirarsa da BBC, hamisu bureka ya ce yakan yi waƙa ne da za ta shafi samari da masu manyan shekaru, sai gashi ta ƙarɓu ta ƙara masa farin jini kuma har ta shiga fagen manyan masu nazarin adabin baka. Ga yadda Farfesa Gusau ya feɗe waƙar Waƙar Jarumar Mata tana da yawan ɗiya aƙalla guda goma sha biyar (15). Waƙar ta zama ruwan dare game duniya a tsakanin mutane tun ma ba Hausawa ba. Hamisu Breaker ya yi wannan waƙa ne da harshen Hausa bisa kari na Kananci. Domin haka, mutane tun ma ba matasa ba sun yi hidimar haddace ta, tare da sassauya ta gwargwadon ƙauna da bukatar kowannensu. Wata matar aure ce da ta ke nuna son mijinta, wani don son kuɗi wani don ƙaunar dabbobi kamar akuya, wani don buƙatar ya samu gida ko mota da sauransu. Ta haka suke hawan waƙar, suna juya ta, ta amfani da kalmominsu amma bisa amo da yanayin rerawarta da kuma raujinta. 2.0 Saƙo ko Tarken Waƙar 2.1 Gundarin Turke Babban saƙon da wannan waƙa ta ke ƙunshe da shi, shi ne nuna tsantsar soyayya irin wadda ta ke wanzuwa tsakanin masoyi da masoyiyarsa, wadda kuma bisa yawanci takan zama mutu ka raba ne. Soyayyar masoyi zuwa ga masoyiyarsa ya ratsa wannan waƙa tun daga ɗanta na farko har kuwa zuwa ƙarewarta a ɗa na 15. Wannan waƙa tana ɗauke da kalmomi masu fizgar zuciya, kuma masu sakaya zance bisa hikima da adonta masoyiya. Kuma waɗannan kalmomi da aka zaɓo masu bayyana soyayyar masoyi ga masoyiyarsa ne waɗanda suke tafiya tamkar sautin jirgin ƙasa a yayin da ya darkako hanya. 2.2 Muhallan Turke na waƙar: A wasu misalai na muhallan turke na wannan waƙa su ne inda ɗa na 4 da ɗa na 5 suke faɗin: Jagora: Tilas ganin mu tilas barinmu, : Ƙaunarki tun da nai nisa, : Sam ba batun na fasa ko za

Continue reading

Wakata ta taba ceto wata budurwa daga mutuwa inji Nura m Inuwa

Nura M Inuwa, na ɗaya daga cikin mawaƙan zamani wanda za a iya cewa ya shahara a ƙasar Hausa, kuma ya yi wakoƙi musamman na soyayya da dama. A wata tattaunawa da BBC ta yi da mawaƙin a ShafinInstagram da Facebook, mawaƙin ya bayyana cewayafara waƙa ne tun a 2007, kuma ya fara ne da waƙarsiyasa. Kamar yanda BBC ta ruwaito A cewarsa, a halin yanzu waka ta zama sana’a, kuma hanya ce da zai iya isar wa mutane sako musamman idan ya ga ɓarna sai ya gyara, Ya ce wakokinsa da dama sun kawo sauyi, domin akwai wata waƙarsa mai suna ‘Ga Wuri Ga Waina‘ wadda a ciki ne ya yi magana kan makomar wanda ya kashe kansa. Ya ce a sakamakon haka “akwai waɗanda suka kira ni suka ce na yi ceto, ma’ana na ƙwaci wata yarinya daga halaka, tana ƙoƙarin halaka kanta ta ji waƙar ‘Ga Wuri Ga Waina‘ ta bari” Mawaƙin ya ce akwai waƙarsa ta Tambihi wadda a sakamakon haka ne wani mahaifi da ya yi niyyar yi wa ‘yarsa auren dole ya daina. A irin waƙoƙi masu isar da saƙo dai da Nura ya yi akwai ta ‘Dafin So, wadda ya ce “a waƙar na yi maganganu daban-daban wanda akwai wanda ya kira ni ya ce a dalilin wannan har ya yi fushi matarsa har ta yi yaji, don haka abin da na faɗi na matsayin da so yake da shi, hakan ya ja suka yi sulhu ya dawo da abarsa.” Nura ya bayyana cewa duk a cikin waƙoƙi ya fi son waƙar soyayya, sakamakon babu abin da ya fi so fiye da soyayya a rayuwarsa. Ya bayyana cewa ya yi waƙoƙi da dama tun bayan da ya fara waƙa, amma waƙar da ya fi so ko kuma ta zama bakandamiyarsa ita ce Rigar Aro. A hirar da aka yi da shi, ya kuma bayyana dalilin da ya sa ba a cika ganinsa a cikin fina-finai ba, ya ce “ni mutum ne wanda ina so in ɗauki layi guda ɗaya, in ba shi ƙarfi, ni shi na zaɓa, ni ba ni da ra’ayin fim”. Inji Nura HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Innalillahi wa inna ilaihirrajuun || Ansamu Yawai Mata Masu Cikin Shege Bayan Rufe Makarantu

Innalillahi wa inna ilaihirrajuun Ansamu yawaitar matan da suke samun cikin shege bayan rufe makarantu, sabida bullar korona, Jami’ai a Kenya sun ce ana samun karuwar ‘yan matan da ke yin ‘cikin shege’ a kasar, musamman tun bayan sanya matakan takaita zirga-zirga sakamakon barkewar annobar cutar korona a watan Maris.kamar yanda BBC ta ruwaito, Wasu bayanai da ma’aikatar lafiya ta saki sun nuna cewa a yanki daya kawai an samu ‘yan mata dubu hudu da suka yi ciki tun farkon shiga shekarar nan. An rufe makarantu a fadin kasar a tsakiyar watan Maris a wani bangare na daukar matakan kariya da gwamnati ta yi. Hukumomin sun nuna damuwa cewa a mafi yawan lokuta dangin ‘yan matan ne ake samu da hannu a lamarin. Jami’ai sun kuma nuna fargabar cewa yawan na iya fin haka saboda ba a faye bayar da rahotanni kan cikin ‘yan mata ba. Shugabannin siyasa a yankunan Kenya 47 sun nemi gwamnati da ta yi bincike kan karuwar adadin. Kenya ce take da mafi yawan ‘yan matan da ke yin ciki a duniya, inda ake samun haihuwa 82 daga cikin 1,000. HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

wani babban ma’aikaci zai shafe shekaru 16 a kur kuku sakamkon cutar zawarawa

Wani babban ma’aikacin gwamnati zai shafe sama da shekaru shaida a gidan kur kuku sakamakon cuta da yaudarar zawarawa, Kotu ta daure wani mutumi mai suna Ramat Mohammed bayan an same shi da laifin damfarar zaurawa 194. Ramat Mohammed wanda aka fi sani da Gaddafi, zai shafe shekaru 16 a gidan kurkuku. A ranar Talata, 16 ga watan Yuni, 2020, Alkali Umaru Fadawu na babban kotun tarayya da ke Borno, ya kama Ramat Mohammed da laifin damfarar wadannan Bayin Allah, ya karbe masu N781, 000, 000. Kamar yadda hukumar EFCC ta bayyana, Ramat Mohammed ya yi aiki a matsayin malamin shari’a a gwamnatin jihar Borno. Alkali ya samu wannan mutumi ne da laiffuka biyu na damfara da sata. Mohammed ya yi amfani da sunan wani mutumi inda ya rika saidawa mata wani kati da sunan kungiyar NGO mai zaman kanta. Wannan mutumi ya saida katin rabon abinci da sunan kungiyar Action Against Hunger, inda aka haka ya tara N781, 800, 000 daga hannun zaurawa kusan 200. A karshe dubunsa ta cika, yayin da EFCC tayi ram dashi kamar yanda jaridar legit ta ruwaito, RrMata 40 da aka nemi a damfara su na karatu ne a wata makarantar islamiyya mai suna Fissabi-lillah da ke garin Auno a cikin karamar hukumar Konduga, jihar Borno. Wannan aiki da Ramat Mohammed ya yi ya ci karo da sashe na 1(1)a na dokar damfara da sata na shekarar 2006. .A lokacin da aka karanta masa laifinsa, wanda ake zargin ya amsa cewa bai da gaskiya. A dalilin haka ne Alkali Umaru Fadawu ya yanke masa hukuncin daurin shekara takwas na kowane daga cikin laifin. Alkalin ya ce shekarun zaman kason za su yi aiki ne a lokaci guda. Kotu ta kuma bukaci wanda aka kama ya biya adannan matan islamiyya kudinsu har N781,800.00   HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

zanga zangar da akeyi a arewacin Najeriya zai iya bata aikin da sojoji keyi inji Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zanga-zangar da ake yi don nuna adawa da kashe-kashen da ke faruwa a arewacin Najeriya na iya ɓata ayyukan da sojoji ke yi a yankin. A wata sanarwa da fadar gwamnatin kasar ta fitar a ranar Talata mai dauke da sa hannun mai taimaka wa Shugaba Buhari kan yada labarai Malam Garba Shehu, shugaban ya yi kira ga al’ummar jihar Katsina da kar su fitar da rai kan sojoji wadanda ake da yakini a kansu shekaru da dama da suka wuce na yadda suke shawo kan rikice-rikice. Kamar yanda jaridar BBC ta ruwaito, Sanarwar ta kuma bai wa ‘yan kasar tabbacin cewa dakarun sojinta za su iya magance matsalar fashi da makami da ta’addanci, inda ta ce a kara hakuri ana daukar matakan da suka dace na kare rayukan ‘yan kasar. Hakan na zuwa ne bayan da a ranar Talatar da safe wasu kungiyoyi da dama suka fatsama kan tituna a birnin Katsina da ke arewacin Najeriyar inda suka yi kira a dauki mataki game da kashe-kashen da ke faruwa a yankin. Masu zanga-zangar, mai taken #ArewaIsBleeding a Turance, wato ‘Jini yana kwarara a Arewa’, sun bayyana matukar bacin ransu kan halin ko-in-kula da suke zargi gwamnatocin kasar na yi kan yawaitar kashe-kashe a yankin. Sun ce za su gudanar da irin wannan zanga-zanga a jihohi 19 da ke arewacin kasar don matsa lamba ga gwamnati ta dauki matakin da ya dace kan masu kashe-kashen. Sanarwar ta ce Shugaba Buhari – wanda ya bayar da umarnin samar da wata tawaga ta musamman ta ‘yan sanda da sojoji don magance rashin tsaro a jihohin Naija da Katsina da Sokoto da Zamfara, ya ba da tabbacin cewa za a kara sa ido, ta hanyar yin shawagi da jiragen sama da daddare, wadanda tuni aka samar da su karkashin shirin arangamar da sojoji ke yi a yankin mai taken “Operation Accord”. An kaddamar da wannan runduna ta arangamar ne mako uku da suka gabata. ”Sojojin Najeriya sun nuna za su iya a baya kuma za su sake tabbatar da cewa a wannan karon ma za su iya shawo kan matsalolin da ake fuskanta,” in ji shugaban kasar a cewar sanarwar. Shugaba Buhari ya kuma bai wa al’ummar jihar Katsina hakuri da neman su bayar da goyon baya ga ayyukan soji da ke faruwa a jihar. A karshe ya mika sakon jajensa da ta’aziyya ga wadanda suka rasa masoyansu. ”An gano manyan dazuzzuka a arewa maso yammacin kasar inda ya zama yankin da ‘yan fashi da makami ke buya. Sojoji za su lalata wadannan dazuzzuka,” a cewar shugaban. Rahotanni sun nuna cewa makon da ya gabata kadai ‘yan bindiga da mayakan Boko Haram sun kashe mutum fiye da 100 a hare-haren da suka kai jihohin Katsina da Borno. Gwamnatin kasar ta sha cewa jami’an tsaro suna magance matsalar tana mai cewa galibin hare-haren da ake kai wa na gyauron ‘yan bindiga ne, ko da yake ‘yan kasar na cewa hakan ba gaskiya ba ne. Ranar Litinin kungiyar kare

Continue reading

Alaka Me Tsami Na Kara Bayyana || Yanzu Yanzu Ganduje Yayi Watsi Da Rahoton Gwamnatin Tarayya

Alaka Me Tsami Na Kara Bayyana || Yanzu Yanzu Ganduje Yayi Watsi Da Rahoton Gwamnatin Tarayya, kamar yanda BBC ta ruwaito, Gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje, ya musanta rahoton gwamnatin tarayyar kasar da ya gano cewa cutar korona ce ta yi ajalin kashi 50 zuwa 60 cikin 100 na mutanen da suka mutu a baya bayan nan. A wata sanarwa da ya fitar, Abba Anwar, mai magana da yawun Gwamna Ganduje, ya ce kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa domin yin bincike kan mace-mace ya gano cewa kusan kashi kashi goma sha shida cikin dari ne suka mutu sanadin korona. Gwamnan ya ambato kwamitin yana cewa: “Mutum 255 cikin 1604 da suka mutu, wato kashi 15.9… ne suka mutu sanadin cutar korona. Wasu daga cikin mace-macen suna da alaka da rashin samun magunguna da kuma dakatar da harkokin rayuwa da na kasuwanci saboda fargabar annobar korona.” A makon jiya ne Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya bayyana wa manema labarai a Abuja cewa binciken da tawagar gwamnatin tarayya ta gudanar game da ƙaruwar mace-mace a jihar Kano, Hakanmay nuna cewa mutum 979 ne suka mutu a kwanannan sanadin mace macen da ba a saba gani ba a jihar, kamar yanda BBC ta ruwaito, A watan Afrilu Shugaba Muhammadu Buhari ya aika kwamitin na musamman zuwa Kano don gano sanadin yawaitar mace-macen, sannan ya sanya dokar hana fita ko da yake daga bisani Gwamna Ganduje ya kyale mutane su ci gaba da fita a wasu ranaku a duk fadin jahar, HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Tirkashi || yanzu yanzu jamb ta kayyade makin da yakamata ku samu

Hukumar shirya jarabawar shiga Jami’a da wasu makarantu na gaba da sakandire JAMB, ta kayyade yawan makin da sai dalibai sun samu kafin samun nasarar ci gaba da karatunsu. Hukumar JAMB ta amince da 160 a matsayin maki mafi karanci don samun gurbin karatu a jami’oin gwamnati da ke fadin tarayya kasar nan a bana. An kayyade wannan maki a yayin taron tsara hanyoyin shiga makarantun gaba da sakandire karo na 20 da ta gudanar a ranar Talata. Taron wanda aka gudanar da shi ta hanyar kiyaye dokar nesa-nesa da juna, hukumar ta kuma kayyade 140 a matsayin mafi karancin makin samun damar shiga jami’o’i masu zaman kansu. Kamar yanda jaridar legit ta ruwaito, Haka kuma hukumar JAMB ta kayyade 120 a matsayin mafi karancin makin shiga makarantun polytechnic na gwamnati. Sai kuma 100 na kwalejin ilimi da makarantun koyon sana’a. Yayin taron wanda shugaban Hukumar JAMB na kasa, Ishaq Oloyede ya jagoranta, ya nemi dukkanin makarantun gaba da sakandire a kan kada kudin tantance dalibai ya haura naira 2000. Sai dai kamar yadda aka saba, har yanzu jami’o’i na da damar kara yawan makin ga dalibai fiye da adadin da hukumar JAMB ta kayyade. Oloyede ya bayyana cewa, jami’oi da makarantun gaba da sakandire sun bai wa dalibai 612,557 damar ci gaba da karatunsu cikin dalibai 1,157,977 da suka zana jarabawar JAMB a bara. Da ya ke ci gaba da gabatar da jawabai, Oloyede ya nemi makarantun gaba da sakandire su ci gaba da aiwatar da shirin daukan dalibai a bana bisa ka’idojin da aka amince dasu. Hukumar ta sanar da wannan mataki bayan kammala babban taro na masu ruwa da tsaki kan sha’anin ilimi a Najeriya wanda ministan ilimi Adama Adamu ya halarta. Jaridar The Sun ta ruwaito cewa, Chukwuemeka Nwajiuba, karamin ministan ilimi shi ne wakilci Adamu Adamu a taron da aka gudanar. Ministan ya nemi hukumar JAMB da ta yi la’akari da daliban da su gabatar da kyakkyawan sakamako ko da shaidar su ta kammala karantun sakandire (SSCE) ba ta bana bace.         HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading