An Bayyana Sunan Shugaba Buhari Da Shekau A Matsayin Manyan Musulman Duniya

Wata sabuwa kenan An bayyana shugaba Buhari da shugaban ‘yan Boko Haram Abubakar Shekau a cikin jerin manyan Musulmai na duniya ko mene dalilin hakan oho An bayyana sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin mutum na 17 a cikin jerin Musulmai da suka yi suna a duniya – Bayan shugaban kasar an bayyana shugaban ‘yan ta’adda na kungiyar Boko Haram a matsayin na bakwai a cikin manyan Musulmai ‘yan ta’adda na duniya – Sai kuma Sarkin Kano Muhammad Sanusi II da kuma hamshakin mai kudin nan Alhaji Aliko Dangote su ma sun fito a cikin jerin mutanen Wannan ita ce shekara ta hudu da aka bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sarkin Musulmai, Muhammad Sa’ad Abubakar III, da kuma shugaban kungiyar ‘yan ta’addar nan ta Boko Haram, Abubakar Shekau, a cikin jerin manyan Musulmai na duniya. Wannan ya fito a wani rahoto da aka fitar akan Musulmai a wata mujalla mai suna Muslim500 da aka fitar ta shekarar 2020, inda aka buga mujallar domin a ware manyan Musulmai na gari da kuma na banza a cikin al’ummar Musulmai, wanda aka saki a jiya Laraba 2 ga watan Oktobar nan. Buhari ya fito a mutum na 17 a cikin jerin manyan Musulmai, inda shi kuma Sarkin Musulmi ya zo a matsayin na 20, sai dai shi kuma shugaban kungiyar ‘yan ta’adda ta Boko Haram Abubakar Shekaru ya zo a matsayin na bakwai a cikin jerin Musulmai ‘yan ta’adda na duniya, haka kuma hamshakin mai kudin nan na Najeriya Alhaji Aliko Dangote da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II sun fito a cikin jerin mutanen. Wasu daga cikin manyan Musulman na duniya sun hada da dan wasan kwallon kafar nan na kasar Egypt kuma dan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Mohammed Salah, sai kuma shugaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane da kuma dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Paul Pogba. A yadda shafin na Muslim500 ya ruwaito ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kokari matuka wajen yaki da cin hanci, farfado da tattalin arziki da kuma tsaro a Najeriya. Buhari dai wanda ‘yan adawa ke faman zargin shi da nuna bangarenci da kuma banbancin addini, yanzu dai ya fito a cikin jerin manyan mutane na duniya. Sarki Sanusi dai ya maye gurbin kawun shi marigayi Sarkin Kano Dr. Ado Bayero fatan mu dai anan shine Allah kasa mucika da imani HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading