Wannan Shine Kazafun Da Akayiwa Sarkin waka kafun akamashi a gidansa

Hukumar tace fina finai tana zargin sarkin wakar sarkin kano Naziru m Ahmad da yin studio acikin gidan bayan bunciken da akayi ba a samu hakan ba sai labari ya canza,   idan baku manta ba ankama sarkin wakar sarkin kano acikin makonnan me karewa bisa zargin ya saki wasu wakoki ba bisa ka ida ba anje har gida an tafi da sarkin wakar, futaccen dan wasan barkwancinnan mustafa naburaska ya saki wani faifan bidiyo da cikakken bayanin yanda akayi, naburaska yace da farko kotu tabada umarnin ashiga gidan naziru a bincika sabida ana zargin yayi studio acikin gidan babisa kaida ba sarkin waka ya kirani a waya ya gayamun cewa jamian tsaro sunzo gidansa domin yin buncike sai nagaya masa cewa idan har jamian tsaro sunzo gidan mutun buncike to ya basu hadin kai danaje dani dasu muka shiga wannan gida akai buncike babu studio ko daya acikin wannan gida jamian tsaro suka futo suka shedawa jamaar waje cewa sun buncika babu studio acikin wannan gida daganan suka kira hukumar tace fina finai suka ce musu sunyi buncike babu komai agidan wannan bawan Allah naburaska ya kara da cewa wannan abu da akeyi badan Allah akeyin sa ba kuma da mukaje state cid sai labari ya canza sai wani jamiin hukumar tace fina finai ya rububuta cewa wai ana zargin nazirun da sakin wakoki ba bisa ka ida ba sai mukace agaya mana wakokin sai aka fada mana wasu tsofafun wakokin sa guda biyu, wannan turka turka de an dade anayinta tsakanin hukumar tace fina finai da masu harkar film musamman wadanda ake ganin yan jam iyyar hamayya ne HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading