Tallan Rigar Nono Ya Saka Anayiwa Jaruma Maryam Booth Magan Ganun Batsa

Tallan Rigar Nono Ya Saka Anayiwa Jaruma Maryam Booth Magan Ganun Batsa a shafunta na instagram wasu suna ganin hakan bai dace ba Maryam Booth ta sha zagi a wajen masoyanta akan tallar rigar nono da tayi ashafunta na instagram Fitacciyar Jaruma Maryam Booth tasha tofin Allah tsine ga mabiyanta na shafin Instagram Jarumar ta sha bakaken maganganun ne bayan ta wallafa wasu rigunan nono a shafinta inda take tallatasu akan kudi naira dubu goma sha shida babu ragin ko sisi Mabiyanta da yawa sun zage ta akan wannan kaya da ta wallafa, inda wasu kuma suka dinga yi mata nasiha akan cewa hakan da ta yi bai kamata ba kuma bai dace ba amma wasu suna ganin hakan ba laifi bane musamman yan uwanta mata, Jaruma Maryam Booth ta sha kalamai marasa kan gado na rashin da’a daga mabiyan shafinta na Instagram sakamakon tallata wasu samfurin rigunan mama da tayi a shafin ta akan zunzurutun kudi har naira dubu goma sha shida (N16,000), kowacce guda daya. Jarumar dai ta wallafa hoton rigunan ne a shafinta inda ta kuma rubuta a kasa da harshen turanci cewa rigar nono La Senza ta sayarwa akwai lamba 36C da kuma 34D, farashinsu dubu goma sha shida duk guda daya. Jim kadan da wallafa wadannan hajoji nata sai ta fara shan martani inda mafi akasarin masu korafin tsadar rigar nonon mata ne, inda wasu ke cewa rigar nonon 16,000 zasu siya kuma su dora mata wata rigar a saman ta, wata budurwa kuwa cewa tayi watakila ko tayi kuskure ne tana nufin dozen ne a wannan farashin. Sai dai jarumar ta mayar da martani da cewa ita wannan rigar mama ta La Senza haka kudinta yake ga wanda ya san farashinta, kowa ya san me tsada ce, sannan kuma ga wanda yake tantama zai iya bincikawa a shafin La Senza na yanar gizo domin tabbatar da farashin na ta. A bangaren samari ‘yan bana bakwai kuwa abin ya kazanta domin maganganu na rashin da’a suka dinga yiwa jarumar. Wasu daga cikin mabiyan nata masu kaifin hankali sun fadakar da ita cewa a matsayinta na mace kuma sananniya bai kamata ta tallata irin wannan kayan sawar mata na ciki ba wanda mafi yawanci ansan mata da boye su zai fi kyau ta sai da su a shago ko rumfa inda matan za su je su siya amma ba ta wallafa a shafinta HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Idan Dagaske kina son Mijina Kofa A bude take Inji Amaryar Adam a Zango

Idan dagaske kina son mijina kofa abude take inji amaryar adam a zango lalle tazama yar aljanna sabida ba macen dazata iya haka a wannan zamanin Amaryar da jarumi Adam A Zango ya auro watannin da suka gabata mai suna safiyyawacce akafu sani da sofy ta wallafa wani rubutu a shafinta na Instagram da ya jawo hankalin mutane da yawa Amaryar ta bayyana irin soyayyar da take yiwa mijin nata, sai dai kuma wata yarinya me karfun hali  ta nuna cewa ita ma tana son mijin nata idan za ta yadda ta zama abokiyar zamanta, Abun mamaki amaraya safiyya ba ta yi kasa a guiwa ba ta bayyana cewa kofa a bude take idan har tana so ita ba ta da damuwa akan hakan kunji fa yar aljanna A ‘yan kwanakin nan amaryar fitaccen jarumi Adam A Zango ta wallafa wani hoto na mijin ta inda ta rubuta cikin harshen turanci cewa; “Mijina abin alfahari na ina sonka so mai tsanani,” amaryar ta yi rubutun ne cikin takaitattun harufa. masu ban shaawa kuma da alamun alokacin tana cikin farin ciki matuka Koda ta wallafa wannan hoto da wannan rubutu sai aka samu wata me karfin hali a cikin ‘yan matan dake bibiyar shafinta tayi tsokaci da harshen turanci tana  cewa nima ina son shi dan Allah ki amince in zamar miki abokiyar zama. Ananne fa amarya Safiyya ba ta yi kasa a guiwa ba ta mayar da amsa da cewa kofa a bude take. Sai dai bayan nan kuma Safiyya ta kwafo wannan magana ta waccan yarinya ta sake wallafawa a shafinta na instagram kana ta kara tabbatar mata da cewa kofa fa a bude take. idan har dagaske take Wannan sake wallafa jawabin da tayi sai yasa wasu ke mata martani da cewa maganar ta dame ta ne shi yasa har ta sake kwafo zancen yarinyar ta wallafa saboda kishi na damunta shi yasa ta kasa mantawa. Ga dukkan alamu wannan martani bai yiwa amaryar dadi ba dan haka tayi wani dogon rubutu ta wallafa a shafin nata wanda har ya bawa angon nata dariya shima ya sake wallafawa a shafinsa, sannan ya rubuta a kasa cewa kin sani dariya HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading