Sabuwar Rigima Abba Kabir Yusif Ya Maka Ganduje a Kotu

Abba Kabir Yusuf, mutumin da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kayar a zaben gwamna na shekarar 2019, ya gurfanar da Ganduje a gaban kuliya. Sai dai wannan karon ba batu ne na zargin yin magudin zabe ba. Abba Kabir Yusuf ya shigar da kara gaban kotu yana mai kalubalantar matakin da Gwamna Ganduje ya dauka na mallaka wa wasu fitattun ‘yan kasuwa, otal din Daula da kuma tashar motoci ta Shahuci da ke cikin birnin na Kano. Lauyan tsohon dan takarar gwamnan, Barista Bashir Yusuf, ya ce hakan ya ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya da yake magana kan hakkin mallakar ƙasa ko fili. Sai dai bangaren gwamnati ya ce har yanzu ba su da labarin shigar da karar. Abin da ya faru a kotu Kazalika lauyan Abba Kabir Yusuf ya ce akwai batun bashi na gina layin dogo mai amfani da lantarki da gwamnatin ta shirya ciyowa daga kasar China wanda ya ce idan aka karbo za a jefa Kano a cikin mawuyacin hali na durkushewar tattalin arziki. Sai dai lauyan gwamna wanda kuma shi ne Kwamishina Shari’a na jihar Kano, Barista Musa Lawan, ya ce ko kadan babu kanshi gaskiya a cikin labaran da ake yadawa game da bayar da filayen. Tashar mota da ke Shahuci na cikin wuraren da aka kai kara a kansu.Image caption: Tashar mota da ke Shahuci na cikin wuraren da aka kai kara a kansu. Ya ce an bai wa wani kamfani tashar motar zamani ta Shahuci ne don yin shaguna na zamani da zai sayar da su ga ‘yan kasuwa kamar yadda gwamnatin jihar ta yi a kasuwar Dangauro da ke titin Zaria a Kano. Ya kara da cewar layin dogon kuma tsohon aiki ne domin kuwa sai da gwamnati ta sami amincewar Gwamnatin Tarayya sannan ita kuma gwamnatin China ta bayar da bashin da ake magana a kai. Barista Musa Lawan ya ce otal din Daula ma kwatankwacin hadin guiwa da gwamnatin Kano ta shiga da sauran kamfanoni ne amma ba ta mallakawa kowa shi ba. A cewarsa, hasalima tana duba yiwuwar yadda za a bai wa masu sha’awar zuba jari dama, sannan kasuwar zamani za a samar a wurin kamar dai yadda shi mai kamfanin ya nema. Idan baku manta ba de Abba Kabir Yusif shine dan takarar daya fu kowa farin jini a Najeriya a shekarar 2019 HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Ganduje zai kafa kolejin koyar da dabarun yaki da cin hanci da Rashawa

Ganduje zai kafa kolejin koyar da dabarun yakin cin hanci da Rashawa a jahar sabida yaranmu su kaucewa cin hanci da Rashawa Yaranmu za su samu horon da ya kamata su samu, sannan su kansu ma’aikatan za a horar da su dabarun kaucewa cin hanci da rashawa.” Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya za ta kafa kwalejin horaswa da koyar da dabarun yaki da cin hanci da rashawa karkashin hukumar korafin Jama’a da hana rashawa ta jihar. Tuni majalisar zartar wa ta Kano ta amince da kafa sabuwar kwalejin koyar da dabarun yaki da rashawar a wani mataki na samar da kwararru kuma managartan Jami’an yaki da rashawa a cewar, Barrister Muhuyi Magaji da ke zaman shugaban hukumar hana ayyukan rashawa ta jihar Kano. “Yaranmu za su samu horon da ya kamata su samu, sannan su kansu ma’aikata za a horar da su dabarun kaucewa cin hanci da rashawa.” In ji Barrister Magaji. Shirin na zuwa ne a dai-dai lokacin da masharhanta ke ci gaba da tsokaci dangane da dakatarwar da fadar shugaban Najeriya ta yi wa shugaban hukumar EFCC Ibrahim Mustafa Magu. Ana dai zarginsa ne da laifukan kin yin biyayya da kuma almundahana kan wasu kudade da kadarori. Akwai masu ra’ayin cewa, abin da ya kai ga tuhumar da ake yi wa Ibrahim Magu, ramuwar gayya ce da rashawa ke yi ga masu yakar ta. HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Akwai yiwuwar Ganduje Zai fuskanci Gori Kan Bidiyon Dala a Zaben Edo

Cacar baki ta ɓarke tsakanin manyan ‘yan siyasa biyu game da zaɓen gwamnan jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya. Wani bidiyo na yawo a shafukan sada zumunta inda gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, wanda shi ne jagoran kamfe na PDP a zaben gwamna a jihar Edo yana zolayar gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje cewar ‘dala’ ba za ta yi tasiri ba a zaben. Kalaman na Wike sun kasance martani ga shugaban yaƙin neman zaɓe na APC, wato Gwamna Ganduje wanda bayanai suka ambato shi yana cewa kafin zaɓen gwamnan jihar Edo, ‘za mu kai Wike wurin killace masu cutar korona’. A shekarar 2018 aka wallafa wasu bidiyon gwamna Ganduje yana sunkuma Daloli a Aljihunsa Ko da yake mukarraban Ganduje sun ce bidiyon ba sahihi ba ne. Gwamna Wike, a jawabinsa wajen kaddamar da kwamitin kamfe na PDP a Abuja, ya ce ‘babu wanda zai buɗe mana ido kan zaɓen jihar Edo’. “Na karanta a jaridu cewa Gwamna Ganduje ya ce za a kai ni wajen killace masu fama da cutar korona har sai an kammala zaɓen Edo, shin wa ya kamata a kai cibiyar?,” in ji Wike. Gwamna Wike ya ƙara da cewa abin da bai sani ba shi ne cewa “mu mutanen Neja Delta za mu karɓi dala sannan mu juya masa baya. Ganduje dalarka ba za ta yi aiki ba a Edo”. Batun zaɓen gwamnan jihar Edo na ci gaba da jan hankali sosai a Najeriya musamman tsakanin ‘ya’yan manyan jam’iyyun siyasar ƙasar watau APC da PDP inda kowacce ke kokarin ganin ita ce ta yi nasara. A ranar 19 ga watan Satumba ne za a yi zaɓen tsakanin gwamna Godwin Obaseki na PDP da kuma Fasto Ize Iyamu na APC. Akwai yiwuwar dai gwaman Ganduje zai iya fuskantar Gori na siyasa awajan yayan jamiyyar PDP musamman a jahar Edo, HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Kungiyar Izala Tayi Mubayi’a Ga Sabon Shugaban cin APC

Kungiyar Izala Tayi Mubayi’a Ga Sabon Shugaban cin APC yayin wata ziyara da shugaban izalar sheikh Bala lau, ya kaiwa mai mala buni, Kungiyar Izala de an dade ana zargin ta da marawa gwamnatin APC baya kusan mutane sun dogara ne da rashin magantuwa kan abubuwan da suke faruwa a kasa baki daya, Kowa yasan yanda malaman izala suke daukar zafi kan duk wani abu dayake Faruwa ba dede ba, amma sai gashi suna bun gwamanti sau da kafa musamman ma shugabannin kungiyar, HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

fadar shugaban kasa ta dakatar da Ibrahim magu

Wata majiya me karfi ta nuna cewa fadar shugaban kasa Buhari ta dakatar Ibrahim magu kamar yanda BBC ta bayyana Fadar shugaban kasa ta dakatar da Ibrahim Magu daga shugabancin hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki ta Najeriya EFCC. Wata majiya mai karfi da ta bukaci a sakaya ta daga Fadar shugaban Najeriya ce ta tabbatar wa da BBC Hausa hakan a ranar Talata. A ranar Litinin ne Ibrahim Magu ya bayyana a gaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin bincike kan zargin da ake yi masa na aikata ba daidai ba. Kwamitin – karkashin jagorancin tsohon mai shari’a Ayo Salami – ya gayyaci Mr Magu ne domin jin ta bakinsa kan abubuwan da suka shafi jagorancinsa a hukumar ta EFCC. Kamar yanda BBC ta ruwaito, Wasu majiyoyi a Najeriya sun tabbatar cewa Magu ya kwana a tsare a hannun jami’an tsaro saboda ba a kammala binciken da aka soma ba a ranar Litinin. HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

tonon silili || shin dagaske fantami ya sayawa matansa uku gidaje a Abuja?

tonon silili || shin dagaske fantami ya sayawa matansa uku manyan gidaje masu tsada a Abuja? Ma’aikatar sadarwa ta Najeriya ta musanta wasu labarai da ke ta yawo a kafafen sada zumunta na kasar cewa Minista Dakta Ali Isa Pantami ya sayawa matanshi uku gidaje a Abuja. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar Uwa Suleiman ta fitar ta ce wannan batu ba shi da tushe balle makama. Sanarwar ta ce “labarin jaridar intanet ta Sahara Reporters ta wallafa da ke zargin cewa ministan ya sayawa matansa uku gidajen a Abuja karya ne. Tun da ministan ya kama aiki a bai sayi gida ko daya ba, kuma gidan da yake zaune ciki ya kama shi ne tun a watan Janairun 2017, shekara biyu kenan gabanin ya kama aiki”. sanarwar ta kuma ce sauran gidaje biyun da jaridar ta wallafa ba ma a san daga inda ta samo su ba. Bugu da kari ta yi kira ga al’ummar kasar da su yi watsi da wannan kokarin bata wa Minista Ali Pantami suna da ake kokarin yi HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Ni Ba takardar dala bace da zaka kalmashe kasa a Aljihu – Godwin Obaseki

Ni Ba takardar dala bace da zaka kalmashe kasa a Aljihu wannan kalami bai yiwa magoya bayan Ganduje dadi ba Tu lokacin da aka nada Ganduje a matsayin shugaban komitin yakin neman zaben APC a jahar Edo magoya bayan Godwin Obaseki sukai ta yiwa Gwamna Ganduje martani, Kamar yanda wani dan PDP a jahar maisuna sunday idona ya bayyana cewa shugaban su Godwin Obaseki ba takardar dala bace da Ganduje zai saka acikin Aljihu Tabbas wadannan kalamai basu yiwa magoya bayan APC dadi ba musamman a jahar Edo, Idan baku manta ba wannan kwamiti de zaa rantsar dashi ne a ranar 6 ga wannan wata a babban birnin tarayya Abuja, Amma babban abun tambaya anan shine yaushe maganar dala zata kare? HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Gwamnan Bauchi ya dakatar da sarkin misau

Gwamnan Bauchi ya dakatar da sarkin misau sakamakon tashin hankula da ake samu a yankinsa Gwamnan jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya Bala Muhammad Kaura, ya dakatar da Sarkin Misau, Alhaji Ahmed Sulaiman sakamakon tashin hankali da aka samu a yankin tsakanin manoma da makiyaya. Tashin hankalin a wannan mako, a garin Zadawa da ke cikin karamar hukumar ta Misau, ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum tara da jikkata wasu da dama. Gwamna Bala Kaura ya sanar da dakatar da Sarkin ne yayin kaddamar da wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan rikici mai nasaba da wani fili da ake takaddama a kai. Gwamnan na jihar Bauchi ya kuma dakatar da wasu sarakunan gargajiya masu mukaman hakimi da dagaci a yankin da rikicin ya shafa. Sarkin Misau dai na daga cikin manyan sarakunan gargajiya a jihar ta Bauchi. Tun farko gwamnan ya dakatar da shugaban riko na karamar hukumar ta Misau da wasu manyan jami’an karamar hukumar. Gwamnatin jihar na zarginsu da yin sakaci game da rikicin. Gwamnan ya ce an dakatar da jami’an da sarakunan gargajiyar ne domin bayar da damar gudanar da bincike. Dakatarwar za ta ci gaba da aiki zuwa lokacin da za a kammala bincike. An ba kwamitin binciken da aka kaddamar makwanni uku ya gabatar da rahotonsa. Kawo yanzu ba a kai ga jin ta bakin shuwagabannin da aka dakatar ba. A 2015 ne dai aka nada Alhaji Ahmad Sulaiman Sarkin Misau, bayan rasuwar Sarki Muhammadu Manga. Ba a cika samun rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar ta Bauchi ba idan aka kwatanta da wasu jihohin Najeriya masu fama da irin wannan rikici da ma matsalar ‘yan bidiga. HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

zamuci zaben edo ko da inconclusive ne – Gwamna Ganduje

Zamuci zaben jahar edo ko da inconclusive ne jim kadan bayan nada Ganduje a matsayin shugaban yakin neman zaben gwamnan jahar edo. Jama’a dayawa basuyi mamakin nada gwamna Ganduje a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamna a jahar Edo ba. Musamman yanda ake ganin gwamnan a matsayin wanda ya samu nasara bayan cire tsammani da magoya bayansa sukai, Wani futaccen dan Gandujiyya Abdullahi Abubakr kiru ya bayyana cewa tunda aka nada Ganduje a matsayin shugaban yakin neman zaben osaze ize-iyamu, zasu ci zabe koda da inconclusive ne, Idan baku manta ba wannan kwamiti za a rantsar dashi ne a ranar 6 ga wannan wata damuke ciki a babbar sakatariyar APC a Birnin tarayya Abuja. Nadin Ganduje de a wannan matsayi yasa mutane dayawa a jahar kano zargin cewa dama uwar jam iyya ta kasa tana sane da yanda aka gudanar da zaben kano, Shiyasa ma suke kokarin nada Ganduje a matsayin shugaban yakin neman zaben gwamnan na edo, Lokaci de shine bamu damar sanin dalilin dayasa akai wa Gwamna Ganduje wannan babban mukami a Jam iyyar APC,   HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Jami’iyyar APC za ta iya darewa gida biyu – Bola Tinubu

Jam iftar APC zata iya darewa gida biyu bayan Rikicin gida data da baibaye jamiyyar inji bola Ahmad tinubu   Kasantuwar samun wadansu matsaloli a cikin jam’iyyar APC, inda har ta kai ga musayan yawu a tsakanin shugabannin Jam’iyyar, wanda hakan ya sa a halin yanzu tafiyar jam’iyyar za ta fara tafiya da murya biyu. Daga bisani mun samu rahoto inda Bola Tinubu yake ganawa da manema labarai a garin Legas, bayan sun tashi wani zama na gaggawa da wadansu ba’adin ‘kabilar Yarbawa, ciki har da wadansu ba’adin ‘kabilar Hausawa, don cimma matsayar tafiyar jam’iyyar ta APC a kashin nasu tunanin. Hakan ya ‘kara bude wani sabon fai-fai ne, inda Tinubu yake cewa sune suka yi fadi tashi don ganin an tabbatar da jam’iyyar ta APC, har ta samu karbuwa ga al’ummar Nijeriya’ babu kudanci babu Arewa, kuma farin jinin jam’iyyar APC ta shiga lungu da sako Amma duk da haka Tinubu ya yi wadansu kalamai, inda yake nuna alamun zai yi baya-baya da tafiyar ta APC a halin yanzu, nan da wadansu lokaci kadan, don yin nazari tare da wadansu jiga-jigan Jam’iyyar, inda za su fitar da matsayar su a tafiyar. Kana an samu karin wadansu bayanai inda Tinubu yake cewa dole su yi wa APC kwaskwarima, kodako babu tunanin wadansu masu fada aji a cikin jam’iyyar ta APC, kuma suna da tabbacin idan suka kawo wannan tunanin lallai za a iya samun sauyi na tafiyar ta su. HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading