Alaka Me Tsami Na Kara Bayyana || Yanzu Yanzu Ganduje Yayi Watsi Da Rahoton Gwamnatin Tarayya

Alaka Me Tsami Na Kara Bayyana || Yanzu Yanzu Ganduje Yayi Watsi Da Rahoton Gwamnatin Tarayya, kamar yanda BBC ta ruwaito, Gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje, ya musanta rahoton gwamnatin tarayyar kasar da ya gano cewa cutar korona ce ta yi ajalin kashi 50 zuwa 60 cikin 100 na mutanen da suka mutu a baya bayan nan. A wata sanarwa da ya fitar, Abba Anwar, mai magana da yawun Gwamna Ganduje, ya ce kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa domin yin bincike kan mace-mace ya gano cewa kusan kashi kashi goma sha shida cikin dari ne suka mutu sanadin korona. Gwamnan ya ambato kwamitin yana cewa: “Mutum 255 cikin 1604 da suka mutu, wato kashi 15.9… ne suka mutu sanadin cutar korona. Wasu daga cikin mace-macen suna da alaka da rashin samun magunguna da kuma dakatar da harkokin rayuwa da na kasuwanci saboda fargabar annobar korona.” A makon jiya ne Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya bayyana wa manema labarai a Abuja cewa binciken da tawagar gwamnatin tarayya ta gudanar game da ƙaruwar mace-mace a jihar Kano, Hakanmay nuna cewa mutum 979 ne suka mutu a kwanannan sanadin mace macen da ba a saba gani ba a jihar, kamar yanda BBC ta ruwaito, A watan Afrilu Shugaba Muhammadu Buhari ya aika kwamitin na musamman zuwa Kano don gano sanadin yawaitar mace-macen, sannan ya sanya dokar hana fita ko da yake daga bisani Gwamna Ganduje ya kyale mutane su ci gaba da fita a wasu ranaku a duk fadin jahar, HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Tirkashi || yanzu yanzu jamb ta kayyade makin da yakamata ku samu

Hukumar shirya jarabawar shiga Jami’a da wasu makarantu na gaba da sakandire JAMB, ta kayyade yawan makin da sai dalibai sun samu kafin samun nasarar ci gaba da karatunsu. Hukumar JAMB ta amince da 160 a matsayin maki mafi karanci don samun gurbin karatu a jami’oin gwamnati da ke fadin tarayya kasar nan a bana. An kayyade wannan maki a yayin taron tsara hanyoyin shiga makarantun gaba da sakandire karo na 20 da ta gudanar a ranar Talata. Taron wanda aka gudanar da shi ta hanyar kiyaye dokar nesa-nesa da juna, hukumar ta kuma kayyade 140 a matsayin mafi karancin makin samun damar shiga jami’o’i masu zaman kansu. Kamar yanda jaridar legit ta ruwaito, Haka kuma hukumar JAMB ta kayyade 120 a matsayin mafi karancin makin shiga makarantun polytechnic na gwamnati. Sai kuma 100 na kwalejin ilimi da makarantun koyon sana’a. Yayin taron wanda shugaban Hukumar JAMB na kasa, Ishaq Oloyede ya jagoranta, ya nemi dukkanin makarantun gaba da sakandire a kan kada kudin tantance dalibai ya haura naira 2000. Sai dai kamar yadda aka saba, har yanzu jami’o’i na da damar kara yawan makin ga dalibai fiye da adadin da hukumar JAMB ta kayyade. Oloyede ya bayyana cewa, jami’oi da makarantun gaba da sakandire sun bai wa dalibai 612,557 damar ci gaba da karatunsu cikin dalibai 1,157,977 da suka zana jarabawar JAMB a bara. Da ya ke ci gaba da gabatar da jawabai, Oloyede ya nemi makarantun gaba da sakandire su ci gaba da aiwatar da shirin daukan dalibai a bana bisa ka’idojin da aka amince dasu. Hukumar ta sanar da wannan mataki bayan kammala babban taro na masu ruwa da tsaki kan sha’anin ilimi a Najeriya wanda ministan ilimi Adama Adamu ya halarta. Jaridar The Sun ta ruwaito cewa, Chukwuemeka Nwajiuba, karamin ministan ilimi shi ne wakilci Adamu Adamu a taron da aka gudanar. Ministan ya nemi hukumar JAMB da ta yi la’akari da daliban da su gabatar da kyakkyawan sakamako ko da shaidar su ta kammala karantun sakandire (SSCE) ba ta bana bace.         HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Banajin Dadin Masu Cewa Allah Ya Karawa Mahaifina Nauyin Kasa

Bana Jin dadin yanda wasu jama’a suke cewa Allah ya karawa mahaifina nauyin kasa, domin kafun ya mutu mutumin kirki ne, Idan baku manta ba acikin makonnan ne futaccen jarumin wasan Hausa Ali Nuhu yayi Rashin mahaifunsa Nuhu paloma acan garin Gombe, Mutane dayawa sunyi kokari sosai wajan taya Ali Nuhu Alhini amma wasu dayawa sun rasa ta yadda zasuyi wannan taaziyya sakamakon mahaifun nasa ba musulmi bane , Kowa yasan cewa mutane dayawa suna shiga damuwa musamman idan mahaifun su ya mutu kuma ba musulmi ba sabida magan ganu masu ciwo da suke fuskanta, Nayi kacibus da wani matashi mai suna salim dan asalin jahar katsina yace mahaifunsa ba musulmi bane amma bayan rasuwarsa wadan da nake ganin abokaina ne sune suke cewa Allah ya kara nauyin kasa, Bayan kuma mahaifun nawa kafun ya rasu mutumin kirki ne, babu yanda zanyi dan nasan Addinin musulunci bai yadda kana musulmi ka nema musu gafara ba amma de tabbas lokacin naji babu dadi   HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Yakubu Muhammad ya Badawa Sani Danja Kasa A Ido

Duk aminci da tsananin shakuwa da ke tsakanin jarumin mawakin da jarumi Sani Musa Danja, Yakubu Mohammed ya ce jarumi Ibrahim Mandawari ne ya fi burgesa a harkar fim. Ayayin da BBC ta tattauna da shaharren jarumin kuma mawaki yakubu Muhammad a shafinta na Instagram, Yakubun ya tabo abubuwa da dama da suka danganci siyasa dakuma harkokin fina finan hausa, jarumin yace dama can a jamiyyar PDP suke kuma sun mata ayyuka da dama, Jarumin ya bayyana cewa babban dalilin dayasa bai zage damtse yayiwa PDP waka sosai ba sabida ya kasance ambassador na Hukumar zabe me zaman kanta ta kasa INEC Yakubu Muhammad ya kara da cewa duk kannywood bashi da ubangida shine uban gidan kansa, sai kawai abokan arziki, Sannan ya kara da cewa duk masana antar babu jarumin dayakeburgeshi kamarIbrahim mandawari, HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading