wai shin kunsan ina tsohuwar jaruma Dunbaru tayi kuka dena Ganinta?

Tsohuwar Jaruma Dumbaru de Jaruma ce wacce tayi suna hade da tashe a shekarun da suka gabata,   Jarumar tayi nasarar ruke kambun jarumtar masana antar Hausa film alokacinta, alokacin tayi fina finai da dama wadan da awancan lokacin sukai fice, Amma yawancin fina finan ta da suka karbu tayi sune da marigayi Rabbilu musa Ibro, Alokacin jama’a da dama sun daura alhakin sunan da jarumar tayi a wuyan marigayi Rabbilu musa Ibron tunda alokacin yayi shuhura musamman a bangaran fina finan barkwanci wanda suke kira da camama, Hajara dumbaru de manyan cikin masana antar da kuma kanana da manyan daraktoci da producers suna girmamata sakamakon mace ce ita me san girma sannan kuma bata son raini, Daga cikin fina finan da sukayi tashe nata akwai wani film da sukayi da marigayi Ibron mai suna {Dumbaru masoyiyar Asali} Sai (Dumbaru Chaka Chaka) Bayan Dumbaru de akwai mutane da yawa da ake ganin ta silar Ibro suka samu daukaka kamar su Rabi’u Daushe Suleiman Bosho da irin su Dan Dugaji Da kuma marigayi Kulu sai marigayi katakore da kuma marigayi yautai Allah ya jikansu da gafara, HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading