shin wacce shawara zaku bawa sarkin waka naziru murabus

Shin wacce shawara zaku bawa sarkin waka naziru murabus kan wannan tsohuwar soyayyar Idan baku manta ba de an kwashi soyayya sosai wacce har takusan kaiwa ga aure tsakanin sarkin waka murabus da jaruma Hadiza Gabon Amma bayan rabuwarsu da dadewa anga wasu hotuna suna yawo wanda sukai tallan mudatex tare ana tunanin anya kuwa soyayya bazata dawo danya ba? Shin Wacce shawara kuke tunanin zaku bawa sarkin waka naziru murabus? Kan wannan tsohuwar soyayyar HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Miji Da Mata film ne me Dogon zango wanda zaku fara kallo ranar 1 ga watan October

Miji Da Mata film ne me Dogon zango wanda zaku fara kallo ranar 1 ga watan October Duk wanda yake bibiyar harkokin fina finan hausa yasan cewa ayanzu haka kasuwar film din takoma YouTube Kusan hakan ne dalilin dayasa masu shirya fina finan suka koma shirya fina finai masu Dogon zango wanda akafi sani da series Kamfanin brothers point multimedia ya shirya wani kayataccen film na barkwanci wanda zai fara sakinsa a YouTube ranar 1 ga watan October A tashoshin YouTube kamar haka brothers tv entertainment murnatv kundin nishadi da hausatrust sai kuma hausa series tv Tabbas film din zai nishadantar kwarai dagaske kasancewar manyan jarumai da akasa aciki musamman dan wasan barkwancinnan Suleiman Bosho An hakikance cewar film din zai iya samun karbuwa kasancewarsa ya tabo Abubuwan da suke Faruwa acikin gidajenmu musamman kan kishi Ali Bet de shine ya shirya wannan film sannan malam Aminu Asarab yabada umarnin sa   HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

wasu malaman islamiyyu sun sauke Ganduje daga matsayin khadimul islam

Wasu manyan malaman islamiyya a jahar kano sun sauke gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje daga matsayin khadimul islama Idan baku manta ba tun bayan bullar cutar nan ta coronovirus gwamnatin kano ta dauki matakin garkame makarantun boko da Allo dama islamiyyu da kuma gidajen kwallon kafa dama gidajen da ake gudanar da bukukuwa da kuma kasuwannin jahar kano da nufun kare kai daga wannan annamimiyar cuta, Amma bayan daukar wasu tsawan lokuta ahankali ahankali zaa iya cewar anbude gurare dayawa amma banda makarantun islamiyyu dana boko amma kuma a baya bayannan anbude wasu makarantun bokon da nufun wasu dalibai suje su zana jarabawar WAEC da NECO, Kusan zaa iya cewa wannan daliline yasa wasu malaman islamiyyu bude makarantun su amma sai gashi ana bunsu ana kamawa, Wasu malaman islamiyyu dake tarauni sun bayyana cewa yakamata gwamna Ganduje ya duba wannan Al’amari duba da yanda ake masa lakabi da khadimul islama ya wai wayi makarantun islamiyyu domin suna cikin wani hali, Da muka tattauna da wani malamun islmaiyya wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace daga yau sun sauke Gwamna Ganduje daga matsayin khadimul islama domin har yanzu yakiyin wani hobbasa domin bude wadannan makarantu, Kamar yanda kuka sani de anbude gidan kwallon kafa da gidajen bukukuwa amma kuma haryanzu islamiyyu sun gagata budewa   HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

shin kunsan dinbun masoyan da suka tarbi tsohon sarki sunusi a Kaduna?

Tsohon sarki sunusi ya samu tarbar masoya masu dunbun yawa a ciki da wajan jahar Kaduna Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ziyarci gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai. Wannan ce dai ziyara ta farko da sarkin ya kai wata jiha ta Najeriya tun bayan da ya tare a Legas bayan cire shi daga sarauta a watan Maris. A wani saƙo da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce Sarki Sanusi ya yi alƙwarin yin iya bakin ƙoƙarinsa a matsayinsa na shugaban Jami’ar Kaduna, da kuma mataimakin shugaban hukumar bunƙasa zuba jari ta jihar. Kwanaki kaɗan ne bayan cire sarkin daga sarauta gwamna El-Rufai ya ba Sarkin waɗannan muƙaman   HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Afakallahu zai dauki matakin dakatar da saka film me Dogon zango a jahar kano

Shugaban Hukumar tace fina finai a jahar kano Ismail na Abba Afakallahu zai dauki matakin saka film me Dogon zango a jahar kano, Kamar yadda kuka sani dai zaa iya cewa harkokin film din hausa ayanzu kusan kaso sittin acikin dari zamu iya cewa sun koma kan YouTube kuma yawancin masu saka film a YouTube suna sakashi ne ba tare da Hukumar tace fina finai sun taceshi ba, Kuma yawancin yan downloading suna kwafar wannan film a YouTube su dinga siyarwa da mutane batare da sun siya ba Kusan hakanne yasaka wannan Hukumar daukar wannan mataki amma wasu dayawa daga cikin masu shirya wadannan fina finai sun amunce da wannan mataki na wannan hukuma, A tattaunawar da mukai da shugaban kungiyar masu YouTube na arewa Ali Bet kuma shugaban kamfanin brothers tv entertainment ya bayyana mana cewar Munji dadin wannan mataki da wannan hukuma zata dauka sakamakon mutane suna futa su kashe kudinsu suyi wadannan fina finai kudadensu basa dawowa kawai de sunayine domin su ruke tasharsu amma sai ake samun wasu daga cikin masu downloading suna kwafar wannan film suna sayarwa da mutane batare da sun saya ba amma idan wannan hukuma tashigo to zaa samu wani tsari wanda masu shirya fina finai masu Dogon zango zasu dunga samun kudin shiga Ali bet ya bayyana mana cewa ayanzu kanfaninsa yana shirye shiryen daukan wani film me Dogon zango mai suna MIJI DA MATA wanda yace idan har wannan hukuma ta dauki wannan mataki to hakan zai dinga basu damar kawo fina finai masu kayatarwa A yanzu de zamu iya cewa ana daf da cimma matsaya tsakanin Hukumar tace fina finai da kuma masu YouTube a jahar kano HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Sabuwar Rigima Abba Kabir Yusif Ya Maka Ganduje a Kotu

Abba Kabir Yusuf, mutumin da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kayar a zaben gwamna na shekarar 2019, ya gurfanar da Ganduje a gaban kuliya. Sai dai wannan karon ba batu ne na zargin yin magudin zabe ba. Abba Kabir Yusuf ya shigar da kara gaban kotu yana mai kalubalantar matakin da Gwamna Ganduje ya dauka na mallaka wa wasu fitattun ‘yan kasuwa, otal din Daula da kuma tashar motoci ta Shahuci da ke cikin birnin na Kano. Lauyan tsohon dan takarar gwamnan, Barista Bashir Yusuf, ya ce hakan ya ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya da yake magana kan hakkin mallakar ƙasa ko fili. Sai dai bangaren gwamnati ya ce har yanzu ba su da labarin shigar da karar. Abin da ya faru a kotu Kazalika lauyan Abba Kabir Yusuf ya ce akwai batun bashi na gina layin dogo mai amfani da lantarki da gwamnatin ta shirya ciyowa daga kasar China wanda ya ce idan aka karbo za a jefa Kano a cikin mawuyacin hali na durkushewar tattalin arziki. Sai dai lauyan gwamna wanda kuma shi ne Kwamishina Shari’a na jihar Kano, Barista Musa Lawan, ya ce ko kadan babu kanshi gaskiya a cikin labaran da ake yadawa game da bayar da filayen. Tashar mota da ke Shahuci na cikin wuraren da aka kai kara a kansu.Image caption: Tashar mota da ke Shahuci na cikin wuraren da aka kai kara a kansu. Ya ce an bai wa wani kamfani tashar motar zamani ta Shahuci ne don yin shaguna na zamani da zai sayar da su ga ‘yan kasuwa kamar yadda gwamnatin jihar ta yi a kasuwar Dangauro da ke titin Zaria a Kano. Ya kara da cewar layin dogon kuma tsohon aiki ne domin kuwa sai da gwamnati ta sami amincewar Gwamnatin Tarayya sannan ita kuma gwamnatin China ta bayar da bashin da ake magana a kai. Barista Musa Lawan ya ce otal din Daula ma kwatankwacin hadin guiwa da gwamnatin Kano ta shiga da sauran kamfanoni ne amma ba ta mallakawa kowa shi ba. A cewarsa, hasalima tana duba yiwuwar yadda za a bai wa masu sha’awar zuba jari dama, sannan kasuwar zamani za a samar a wurin kamar dai yadda shi mai kamfanin ya nema. Idan baku manta ba de Abba Kabir Yusif shine dan takarar daya fu kowa farin jini a Najeriya a shekarar 2019 HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Ganduje zai kafa kolejin koyar da dabarun yaki da cin hanci da Rashawa

Ganduje zai kafa kolejin koyar da dabarun yakin cin hanci da Rashawa a jahar sabida yaranmu su kaucewa cin hanci da Rashawa Yaranmu za su samu horon da ya kamata su samu, sannan su kansu ma’aikatan za a horar da su dabarun kaucewa cin hanci da rashawa.” Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya za ta kafa kwalejin horaswa da koyar da dabarun yaki da cin hanci da rashawa karkashin hukumar korafin Jama’a da hana rashawa ta jihar. Tuni majalisar zartar wa ta Kano ta amince da kafa sabuwar kwalejin koyar da dabarun yaki da rashawar a wani mataki na samar da kwararru kuma managartan Jami’an yaki da rashawa a cewar, Barrister Muhuyi Magaji da ke zaman shugaban hukumar hana ayyukan rashawa ta jihar Kano. “Yaranmu za su samu horon da ya kamata su samu, sannan su kansu ma’aikata za a horar da su dabarun kaucewa cin hanci da rashawa.” In ji Barrister Magaji. Shirin na zuwa ne a dai-dai lokacin da masharhanta ke ci gaba da tsokaci dangane da dakatarwar da fadar shugaban Najeriya ta yi wa shugaban hukumar EFCC Ibrahim Mustafa Magu. Ana dai zarginsa ne da laifukan kin yin biyayya da kuma almundahana kan wasu kudade da kadarori. Akwai masu ra’ayin cewa, abin da ya kai ga tuhumar da ake yi wa Ibrahim Magu, ramuwar gayya ce da rashawa ke yi ga masu yakar ta. HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Akwai yiwuwar Ganduje Zai fuskanci Gori Kan Bidiyon Dala a Zaben Edo

Cacar baki ta ɓarke tsakanin manyan ‘yan siyasa biyu game da zaɓen gwamnan jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya. Wani bidiyo na yawo a shafukan sada zumunta inda gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, wanda shi ne jagoran kamfe na PDP a zaben gwamna a jihar Edo yana zolayar gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje cewar ‘dala’ ba za ta yi tasiri ba a zaben. Kalaman na Wike sun kasance martani ga shugaban yaƙin neman zaɓe na APC, wato Gwamna Ganduje wanda bayanai suka ambato shi yana cewa kafin zaɓen gwamnan jihar Edo, ‘za mu kai Wike wurin killace masu cutar korona’. A shekarar 2018 aka wallafa wasu bidiyon gwamna Ganduje yana sunkuma Daloli a Aljihunsa Ko da yake mukarraban Ganduje sun ce bidiyon ba sahihi ba ne. Gwamna Wike, a jawabinsa wajen kaddamar da kwamitin kamfe na PDP a Abuja, ya ce ‘babu wanda zai buɗe mana ido kan zaɓen jihar Edo’. “Na karanta a jaridu cewa Gwamna Ganduje ya ce za a kai ni wajen killace masu fama da cutar korona har sai an kammala zaɓen Edo, shin wa ya kamata a kai cibiyar?,” in ji Wike. Gwamna Wike ya ƙara da cewa abin da bai sani ba shi ne cewa “mu mutanen Neja Delta za mu karɓi dala sannan mu juya masa baya. Ganduje dalarka ba za ta yi aiki ba a Edo”. Batun zaɓen gwamnan jihar Edo na ci gaba da jan hankali sosai a Najeriya musamman tsakanin ‘ya’yan manyan jam’iyyun siyasar ƙasar watau APC da PDP inda kowacce ke kokarin ganin ita ce ta yi nasara. A ranar 19 ga watan Satumba ne za a yi zaɓen tsakanin gwamna Godwin Obaseki na PDP da kuma Fasto Ize Iyamu na APC. Akwai yiwuwar dai gwaman Ganduje zai iya fuskantar Gori na siyasa awajan yayan jamiyyar PDP musamman a jahar Edo, HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Kungiyar Izala Tayi Mubayi’a Ga Sabon Shugaban cin APC

Kungiyar Izala Tayi Mubayi’a Ga Sabon Shugaban cin APC yayin wata ziyara da shugaban izalar sheikh Bala lau, ya kaiwa mai mala buni, Kungiyar Izala de an dade ana zargin ta da marawa gwamnatin APC baya kusan mutane sun dogara ne da rashin magantuwa kan abubuwan da suke faruwa a kasa baki daya, Kowa yasan yanda malaman izala suke daukar zafi kan duk wani abu dayake Faruwa ba dede ba, amma sai gashi suna bun gwamanti sau da kafa musamman ma shugabannin kungiyar, HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

fadar shugaban kasa ta dakatar da Ibrahim magu

Wata majiya me karfi ta nuna cewa fadar shugaban kasa Buhari ta dakatar Ibrahim magu kamar yanda BBC ta bayyana Fadar shugaban kasa ta dakatar da Ibrahim Magu daga shugabancin hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki ta Najeriya EFCC. Wata majiya mai karfi da ta bukaci a sakaya ta daga Fadar shugaban Najeriya ce ta tabbatar wa da BBC Hausa hakan a ranar Talata. A ranar Litinin ne Ibrahim Magu ya bayyana a gaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin bincike kan zargin da ake yi masa na aikata ba daidai ba. Kwamitin – karkashin jagorancin tsohon mai shari’a Ayo Salami – ya gayyaci Mr Magu ne domin jin ta bakinsa kan abubuwan da suka shafi jagorancinsa a hukumar ta EFCC. Kamar yanda BBC ta ruwaito, Wasu majiyoyi a Najeriya sun tabbatar cewa Magu ya kwana a tsare a hannun jami’an tsaro saboda ba a kammala binciken da aka soma ba a ranar Litinin. HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading