wani babban ma’aikaci zai shafe shekaru 16 a kur kuku sakamkon cutar zawarawa

Wani babban ma’aikacin gwamnati zai shafe sama da shekaru shaida a gidan kur kuku sakamakon cuta da yaudarar zawarawa, Kotu ta daure wani mutumi mai suna Ramat Mohammed bayan an same shi da laifin damfarar zaurawa 194. Ramat Mohammed wanda aka fi sani da Gaddafi, zai shafe shekaru 16 a gidan kurkuku. A ranar Talata, 16 ga watan Yuni, 2020, Alkali Umaru Fadawu na babban kotun tarayya da ke Borno, ya kama Ramat Mohammed da laifin damfarar wadannan Bayin Allah, ya karbe masu N781, 000, 000. Kamar yadda hukumar EFCC ta bayyana, Ramat Mohammed ya yi aiki a matsayin malamin shari’a a gwamnatin jihar Borno. Alkali ya samu wannan mutumi ne da laiffuka biyu na damfara da sata. Mohammed ya yi amfani da sunan wani mutumi inda ya rika saidawa mata wani kati da sunan kungiyar NGO mai zaman kanta. Wannan mutumi ya saida katin rabon abinci da sunan kungiyar Action Against Hunger, inda aka haka ya tara N781, 800, 000 daga hannun zaurawa kusan 200. A karshe dubunsa ta cika, yayin da EFCC tayi ram dashi kamar yanda jaridar legit ta ruwaito, RrMata 40 da aka nemi a damfara su na karatu ne a wata makarantar islamiyya mai suna Fissabi-lillah da ke garin Auno a cikin karamar hukumar Konduga, jihar Borno. Wannan aiki da Ramat Mohammed ya yi ya ci karo da sashe na 1(1)a na dokar damfara da sata na shekarar 2006. .A lokacin da aka karanta masa laifinsa, wanda ake zargin ya amsa cewa bai da gaskiya. A dalilin haka ne Alkali Umaru Fadawu ya yanke masa hukuncin daurin shekara takwas na kowane daga cikin laifin. Alkalin ya ce shekarun zaman kason za su yi aiki ne a lokaci guda. Kotu ta kuma bukaci wanda aka kama ya biya adannan matan islamiyya kudinsu har N781,800.00   HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

zanga zangar da akeyi a arewacin Najeriya zai iya bata aikin da sojoji keyi inji Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zanga-zangar da ake yi don nuna adawa da kashe-kashen da ke faruwa a arewacin Najeriya na iya ɓata ayyukan da sojoji ke yi a yankin. A wata sanarwa da fadar gwamnatin kasar ta fitar a ranar Talata mai dauke da sa hannun mai taimaka wa Shugaba Buhari kan yada labarai Malam Garba Shehu, shugaban ya yi kira ga al’ummar jihar Katsina da kar su fitar da rai kan sojoji wadanda ake da yakini a kansu shekaru da dama da suka wuce na yadda suke shawo kan rikice-rikice. Kamar yanda jaridar BBC ta ruwaito, Sanarwar ta kuma bai wa ‘yan kasar tabbacin cewa dakarun sojinta za su iya magance matsalar fashi da makami da ta’addanci, inda ta ce a kara hakuri ana daukar matakan da suka dace na kare rayukan ‘yan kasar. Hakan na zuwa ne bayan da a ranar Talatar da safe wasu kungiyoyi da dama suka fatsama kan tituna a birnin Katsina da ke arewacin Najeriyar inda suka yi kira a dauki mataki game da kashe-kashen da ke faruwa a yankin. Masu zanga-zangar, mai taken #ArewaIsBleeding a Turance, wato ‘Jini yana kwarara a Arewa’, sun bayyana matukar bacin ransu kan halin ko-in-kula da suke zargi gwamnatocin kasar na yi kan yawaitar kashe-kashe a yankin. Sun ce za su gudanar da irin wannan zanga-zanga a jihohi 19 da ke arewacin kasar don matsa lamba ga gwamnati ta dauki matakin da ya dace kan masu kashe-kashen. Sanarwar ta ce Shugaba Buhari – wanda ya bayar da umarnin samar da wata tawaga ta musamman ta ‘yan sanda da sojoji don magance rashin tsaro a jihohin Naija da Katsina da Sokoto da Zamfara, ya ba da tabbacin cewa za a kara sa ido, ta hanyar yin shawagi da jiragen sama da daddare, wadanda tuni aka samar da su karkashin shirin arangamar da sojoji ke yi a yankin mai taken “Operation Accord”. An kaddamar da wannan runduna ta arangamar ne mako uku da suka gabata. ”Sojojin Najeriya sun nuna za su iya a baya kuma za su sake tabbatar da cewa a wannan karon ma za su iya shawo kan matsalolin da ake fuskanta,” in ji shugaban kasar a cewar sanarwar. Shugaba Buhari ya kuma bai wa al’ummar jihar Katsina hakuri da neman su bayar da goyon baya ga ayyukan soji da ke faruwa a jihar. A karshe ya mika sakon jajensa da ta’aziyya ga wadanda suka rasa masoyansu. ”An gano manyan dazuzzuka a arewa maso yammacin kasar inda ya zama yankin da ‘yan fashi da makami ke buya. Sojoji za su lalata wadannan dazuzzuka,” a cewar shugaban. Rahotanni sun nuna cewa makon da ya gabata kadai ‘yan bindiga da mayakan Boko Haram sun kashe mutum fiye da 100 a hare-haren da suka kai jihohin Katsina da Borno. Gwamnatin kasar ta sha cewa jami’an tsaro suna magance matsalar tana mai cewa galibin hare-haren da ake kai wa na gyauron ‘yan bindiga ne, ko da yake ‘yan kasar na cewa hakan ba gaskiya ba ne. Ranar Litinin kungiyar kare

Continue reading

Alaka Me Tsami Na Kara Bayyana || Yanzu Yanzu Ganduje Yayi Watsi Da Rahoton Gwamnatin Tarayya

Alaka Me Tsami Na Kara Bayyana || Yanzu Yanzu Ganduje Yayi Watsi Da Rahoton Gwamnatin Tarayya, kamar yanda BBC ta ruwaito, Gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje, ya musanta rahoton gwamnatin tarayyar kasar da ya gano cewa cutar korona ce ta yi ajalin kashi 50 zuwa 60 cikin 100 na mutanen da suka mutu a baya bayan nan. A wata sanarwa da ya fitar, Abba Anwar, mai magana da yawun Gwamna Ganduje, ya ce kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa domin yin bincike kan mace-mace ya gano cewa kusan kashi kashi goma sha shida cikin dari ne suka mutu sanadin korona. Gwamnan ya ambato kwamitin yana cewa: “Mutum 255 cikin 1604 da suka mutu, wato kashi 15.9… ne suka mutu sanadin cutar korona. Wasu daga cikin mace-macen suna da alaka da rashin samun magunguna da kuma dakatar da harkokin rayuwa da na kasuwanci saboda fargabar annobar korona.” A makon jiya ne Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya bayyana wa manema labarai a Abuja cewa binciken da tawagar gwamnatin tarayya ta gudanar game da ƙaruwar mace-mace a jihar Kano, Hakanmay nuna cewa mutum 979 ne suka mutu a kwanannan sanadin mace macen da ba a saba gani ba a jihar, kamar yanda BBC ta ruwaito, A watan Afrilu Shugaba Muhammadu Buhari ya aika kwamitin na musamman zuwa Kano don gano sanadin yawaitar mace-macen, sannan ya sanya dokar hana fita ko da yake daga bisani Gwamna Ganduje ya kyale mutane su ci gaba da fita a wasu ranaku a duk fadin jahar, HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Tirkashi || yanzu yanzu jamb ta kayyade makin da yakamata ku samu

Hukumar shirya jarabawar shiga Jami’a da wasu makarantu na gaba da sakandire JAMB, ta kayyade yawan makin da sai dalibai sun samu kafin samun nasarar ci gaba da karatunsu. Hukumar JAMB ta amince da 160 a matsayin maki mafi karanci don samun gurbin karatu a jami’oin gwamnati da ke fadin tarayya kasar nan a bana. An kayyade wannan maki a yayin taron tsara hanyoyin shiga makarantun gaba da sakandire karo na 20 da ta gudanar a ranar Talata. Taron wanda aka gudanar da shi ta hanyar kiyaye dokar nesa-nesa da juna, hukumar ta kuma kayyade 140 a matsayin mafi karancin makin samun damar shiga jami’o’i masu zaman kansu. Kamar yanda jaridar legit ta ruwaito, Haka kuma hukumar JAMB ta kayyade 120 a matsayin mafi karancin makin shiga makarantun polytechnic na gwamnati. Sai kuma 100 na kwalejin ilimi da makarantun koyon sana’a. Yayin taron wanda shugaban Hukumar JAMB na kasa, Ishaq Oloyede ya jagoranta, ya nemi dukkanin makarantun gaba da sakandire a kan kada kudin tantance dalibai ya haura naira 2000. Sai dai kamar yadda aka saba, har yanzu jami’o’i na da damar kara yawan makin ga dalibai fiye da adadin da hukumar JAMB ta kayyade. Oloyede ya bayyana cewa, jami’oi da makarantun gaba da sakandire sun bai wa dalibai 612,557 damar ci gaba da karatunsu cikin dalibai 1,157,977 da suka zana jarabawar JAMB a bara. Da ya ke ci gaba da gabatar da jawabai, Oloyede ya nemi makarantun gaba da sakandire su ci gaba da aiwatar da shirin daukan dalibai a bana bisa ka’idojin da aka amince dasu. Hukumar ta sanar da wannan mataki bayan kammala babban taro na masu ruwa da tsaki kan sha’anin ilimi a Najeriya wanda ministan ilimi Adama Adamu ya halarta. Jaridar The Sun ta ruwaito cewa, Chukwuemeka Nwajiuba, karamin ministan ilimi shi ne wakilci Adamu Adamu a taron da aka gudanar. Ministan ya nemi hukumar JAMB da ta yi la’akari da daliban da su gabatar da kyakkyawan sakamako ko da shaidar su ta kammala karantun sakandire (SSCE) ba ta bana bace.         HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Shin yakamata ayi koyi da matan film kuwa? amma sai gashi ance ayi koyi da tsamiya

AishaAliyu Tsamiya ita kadaice macen da yakamata yan mata suyi koyi da ita musamman ta bangaran saka sutura, a Binciken da jaridar hausatrust ta dada yi, Aisha Aliyu tsamiya ita kadaice tafuta zakka acikin dukkanin matan da suke cikiin masana’antar hausa film, kuma ita kadaice yakamata yan mata da matan Aure suyi koyi da ita Musamman a bangaran saka kayan mutunci, Idan kuna bibiyar harkokin fina finan hausa tabbas akwai mata sama da hamsin wadan da jarumai ne acikin wannan masana anta, kowacce idan ka dauko ta sai kaga bazaka iya cewa ayi koyi da ita ba musamman awajan saka kayan mutunci, Aisha tsamiya tabbas ta ciri tuta ko acikin film bazaka ganta ta saka kayan da zasu futar da surar ta ba, zamu iya cewa idan ka tara mutum dari masu kallan film ba lalle ka samu wanda ya taba ganinta da kananan kaya ba, Tabbas yakamata matan film suyi koyi da Aisha tsamiya idan har sun yarda suna koyar da tarbiyya ne, HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

tsohon sarki sunusi yace Najeriya tana shirin fadawa bashin da bazata iya biya ba

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce Najeriya tana shirin fadawa bashin da ba za ta iya biya ba idan ta ci gaba da tafiya da irin salon shugabancinta   Kamar yadda The Punch ta bayyana, Sanusi ya sanar da hakan ne a wani shiri da Emmanuel Chapel ya jagoranta mai taken ‘hanyar shafe illar COVID-19 ga tattalin arziki da kuma hanyar farfadowa’. Ba tun yanzu ba Sanusi yake Kira ga gwamnatin tarayya ba ta rage yawan kudin data ke kashewa don hakan ba zai haidar da da mai ido ba. Kuma ba zai kawo daidaituwar battalion arziki ba, Yace kamata yayi gwamnati ta sake yawan hanyoyin samun kudade ta hanyar kara maaikata a fannonin kwon lafiya da ilimi Sarkin ya kara da cewa yana da tabbacin cewa raguwar kudin shiga a bangarorin man fetur zai iya sawa lila sai munci bashi Dan biyan maaikata albashinsu.tsohon sarki yace dolene a duba Acikin kundin tsarin mulkin dolene mu samu shugaban kasa, da mataimakinsa dolane mu samu minister daga kowacce jaha Dolane my samu shugabanni kana nan hukumomi 774 a fadain kasarnan kuma tilas ne su samu masu bada shawara da kuma mataimaka daban daban Daga wannan kiyasin mun shirya cin bashin da bazamu iya biya ba Ina ta maganar nan na tsawon shekaru a wannan tsarin da muke bi zamu samu daidaito kuwa zuwa wani lokaci? Tsohon sarki yace wannan tattaunawar yakamata mu dinga yi,   HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Rarara ya gwangwaje mawakin kwankwasiyya da dankareriyar mota da kudi Naira miliyan 1

Futaccen mawaki rarara ya gwangwaje mawakin kwankwasiyya da sabuwar mota da kudi limamin miliyan daya, A ranar Juma’a, 12 ga watan Yuni 2020, Fitaccen Mawakin Siyasar Nahiyar Afrika Dauda Kahutu Rarara ya gwangwanje Mawaki Aminu Lawal Dumbulun da Dalleliyar mota kirar kamfanin Peugeot ( Peugeot Continue of Discussion) da kuma kudi kimanin Naira Miliyan daya. Rarara ya yi wa Dumbulun wadannan kyaututtuka sakamakon ficewa da ya yi a siyasar Kwankwasiyya ya dawo Gandujiyya a cikin watan da ya gabata. Dumbulun dai yana a cikin sahun gaba na Mawakan Kwankwasiyya wanda ya rika yin wakoki barkatai a lokacin yakin neman zaben Kwankwaso, ya kuma yi wasu wakokin na jinjina ga tsohon Gwamnan Kano, Eng. Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso. Tun a ranar 30 ga watan Mayu, 2020 mawakin ya bayyana ficewar sa a tafiyar Kwankwasiyya, inda ya bayyana cewa ya dawo tafiyar Gwandujiyya saboda irin yadda ya yaba da halin mawaaki Rarara da kuma dattakon sa na kishin mawaka ‘yan uwan sa. Tuni dai Dumbulun har ya yi sabuwar waka mai taken ‘Ku gayawa Makafi Ku bude Ido akwai Rijiya’ wadda a cikin ta yake yabon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, tare da yin shagube ga mabiya Kwankwasiyya. Fitattun wakokin da Dumbulun ya yi a lokacin da yana Kwankwasiyya sun hada da, Tashi Barci Kasa, Ga Zaki Ma Ci Abokan Gaba, Rugum Da Rugum Sai Tsawa, Mu Makafi Ne Bamu Ganin Kowa. Wannan dai ba shi ne karo na farko da Mabiya Kwankwasiyya suka fara yin mubaya’a a sanadiyyar Dauda Kahutu Rarara ba. HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Asiri Akaimun shiyasa nake saduwa da ‘ya’ya na wa’iyazubillah

7Wani magidanci mai yaya shida, Peter Ayemoba da aka kama saboda yana saduwa da ‘ya’yansa mata biyu ya ce ya fara saduwa da su ne tun bayan rasuwar matarsa wato mahaifiyarsu. Ya kuma ce da amincewar ‘ya’yansa ne ya ke saduwa da su ba tilasta su ya yi ba. Yan sandan jihar Niger ne suka kama Ayemoba a wannan makon bayan yayansa biyu masu shakara 22 da 20 sun yi kararsa zuwa wani dan uwansu da ya kira ‘yan sandan. Da yan sanda suke masa tambayoyi, Ayemoba ya shaidawa yan sanda cewa ya fara saduwa da ‘ya’yansa biyun ne tun bayan da matarsa wato mahaifiyar yayan ta rasu shekara bakwai da suka shude. “Na fara saduwa da ‘ya’ya na kimanin shekara bakwai da suka gabata bayan rasuwar mata ta a 2013. Rasuwarta ya gigita ni ban san lokacin da na fara saduwa da ‘ya’ya na ba. “Rasuwar mata ta ya rikita ni har ta kai ga ban san abinda na ke yi ba. Ina zargin wani ne ya min asiri saboda abinda na rika aikatawa shekara bakwai da suka wuce ba aikin hankali bane. “Bayan rasuwar mata ta na shaku da yaya na har ta kai ga na fara saduwa da su. Ba zan iya fadin dalilin da yasa na yi wa ‘ya’ya na haka ba. Kawai dai zuciya ta tana raya min cewa ba ni ne mahaifi na farko da ya fara saduwa da ‘ya’yan sa ba,” inji Ayemoba. Ya cigaba da cewa, “Bayan rasuwar mata ta ne naji na fara shaawar yaya na. Na kan je dakinsu muyi wasa daga nan kuma muka fara saduwa amma da amincewarsu. “Duk lokacin da suka nuna ba su so, na kan fada musu cewa ina kokarin ganin mun shaku ne tunda mahaifiyarsu ta mutu. “Wasu lokutan na kan yi barazanar zan kashe kai na idan ba su bari na sadu da su ba. Wata rana nayi musu misali da Lot a Bible da ya sadu da ‘ya’yansa kuma Allah bai hukunta shi ba. Na fada musu ba laifi bane shiyasa aka rubuta a Bible.” Ayemoba ya ce matarsa ta biyu da ‘ya’yansa maza hudu ba su san abinda ke faruwa tsakaninsa da yayansa mata ba. “Yaya na mata sun matsa min na sake aure amma duk da haka na kan sadu da su a duk lokacin da na samu dama. Akwai buktar in tafi in nemi taimako don abinda na aikata ba lafiya bane,” in ji shi. A cewarsa, da yardar ‘ya’yansa mata ya ke saduwa da su. “Da amincewarsu muke aikata abinda muke yi. Abinda ke bani mamaki shine tsawon shekarun da muka yi muna saduwa cikin farin ciki. Kwatsam kawai sai suka yi kara ta wurin dan uwan mu shi kuma ya gayyato ‘yan sanda. “Nayi mamakin abinda suka yi, wata kila dai tura ta kai bango ne saboda haka a zartar min da hukuncin da doka ta tanada.” Yan sanda sun ce za a gurfanar da shi a kotu nan ba da dadewa ba.   HausaTrustThe admin user

Continue reading

tonon silili || Korona ta Haddasa Rikici a fadar shugaban kasa Buhari

Yanda cutar korona take kokarin kawo babban rikici a fadar shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari Bayan dawowar dan uwan Buhari daga wata tafiya daya yi   Kamar yadda majiya daga jami’an tsaro ta bayyana, an samu karantsaye a fannin tsaro a fadar shugaban kasa da ke Abuja a daren Alhamis. Aisha Buhari tare da ADC dinta, Usman Shugaba sun yi kokarin saka karfi wajen tilasta mataimakin shugaba kasa na musamman, Sabiu Yusuf don killace kansa. Majiya daga gidan gwamnatin tarayyar ta sanar da ThisDay cewa rikici ya fara ne bayan Sabiu, dan uwan shugaba Buhari ya dawo daga Legas. Gidansa na kusa da fadar shugaban kasa amma sai bai killace kansa ba bayan dawowa daga tafiyar da yayi. Kamar yadda majiya daga jami’an tsaro ta bayyana, an samu karantsaye a fannin tsaro a fadar shugaban kasa da ke Abuja a daren Alhamis. Aisha Buhari tare da ADC dinta, Usman Shugaba sun yi kokarin saka karfi wajen tilasta mataimakin shugaba kasa na musamman, Sabiu Yusuf don killace kansa. Majiya daga gidan gwamnatin tarayyar ta sanar da ThisDay cewa rikici ya fara ne bayan Sabiu, dan uwan shugaba Buhari ya dawo daga Legas. Gidansa na kusa da fadar shugaban kasa amma sai bai killace kansa ba bayan dawowa daga tafiyar da yayi. Dogaro da dokokin dakile annobar korona, majiyar ta ce uwargidan shugaban kasa, Zahra, Halima da Yusuf Buhari sun samu rakiyar wasu jami’an tsaro har da ADC dinta zuwa gidan Sabiu a daren Alhamis. Bayan isarsu ne suka bukaci Sabiu wanda ake kira da Tunde, da ya killace kansa na kwanaki 14 don kada ya kawo musu annobar cikin iyalan . Wannan lamari kuwa ya jawo sa’in’sa tsakaninsu inda Sabiu ya ce ba shine hadimi na farko da ya fara zuwa Legas ya dawo ba. Hatta sabon shugaban ma’aikatan fadar, Farfesa Ibrahim Gambari na zuwa Legas duk kwanakin karshen mako kafin ya samu matsuguni a Abuja. A don haka yake mamakin yadda suka tsananta masa da sai ya killace kansa bayan ziyarar matarsa da yayi bayan ta haihu. Sabiu Wanda aka fi sani da tunde ya samo asalin sunan sa ne daga tsohon mataimakin shugaba Buhari a mulkin soja Shigarsa gida ke da wuya bayan dawowarsa uwargidan shugaban kasa Buhari Aisha tashiga gidan ita da yayanta suka dinga cin zarafinsa   Wata majiya daga fadar shugaban kasa wacce ganauce ba jiyau ba tace sabiu ya tsallake katangar gidan sakamakon harbin da ADC din Aisha suka dingayi a farfajiyar gidan Daga bisani tunde ya samu shiga gidan mamman daura inda ya kwana a gidan zuwa wayewar gari Jaridar thisday ta gani cewa sufeta janar din kasar ya bada umarnin damke ADC din Aisha din bayan rahoto daya samu na samun harbi a fadar shugaban kasar,   HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Wai Meyasa Gwamna Zulum yana neman yiwa Buhari fintinkau a yawan masoya?

Waishin meyasa gwamna zulum yake neman yiwa Buhari fintinkau ta fuskar magoya baya? Musamman a arewacin Najeriya Gwamnan jahar Borno Barista umara zulum gwamna ne wanda za a iya cewa ya samu gagarumar Nasara a cikin gwamnonin Najeriya gaba daya , Gwamna zulum yana sake samun magoya baya a arewacin Najeriya harma da kudancin Najeriya, Gwamnan za a iya cewa ayanzu yana neman yiwa shugaba Buhari funtun kau ta fannin masoya domin yanzu wasu dayawa na ganin cewa gwamna zulum yafu Buhari tausayin talakawa, Tabbas shugaban kasa Buhari yana da babban kalu bale akansa na rasa masoya a arewacin Najeriya Zulum yana sake samun shedar alummar jahar sa ta bangaran taimako da tausayi da nuna halin damuwa akan yanayin da talakawansa suke ciki, A sabida hakane ma wasu suke ganin gwamna zulum zai iya darewa kan mulkin Najeriya idan har ya samu nasarar samun goyon bayan wasu kusoshi a Najeriya, Amma fa tabbas ba lalle zulum ya samu wannan goyon bayan ba sakamakon tausayin talakawa dayake nunawa a fili   HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading