shin kunsan wani sirri da baku sani ba game da nafisa Abdullahi?

Shin kunsan dalilin dayasa nafisa Abdullahi tazama daya daga cikin jerin yan matan da ake ji dasu a masana antar kannywood Jarumar de ta taka rawa a baya sosai a fagen fina finan hausa kuma tana daya dagacikin manyan jarumai da kamfanin FKD yake ji dasu, Nafisa Abdullahi de macece me hakuri a zahiri wacce tana daya daga cikin wadan da yan kallo suke mata kallon shuru shuru ce ita, Sannan jaruma ce wacce take zagewa wajan taka dukkanin wani rol da aka bata, Sannan ta taba soyayya da futaccen jarumi Adam a zango soyayyar da ta kusa kaisu ga aure, HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

tonon silili || shin dagaske fantami ya sayawa matansa uku gidaje a Abuja?

tonon silili || shin dagaske fantami ya sayawa matansa uku manyan gidaje masu tsada a Abuja? Ma’aikatar sadarwa ta Najeriya ta musanta wasu labarai da ke ta yawo a kafafen sada zumunta na kasar cewa Minista Dakta Ali Isa Pantami ya sayawa matanshi uku gidaje a Abuja. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar Uwa Suleiman ta fitar ta ce wannan batu ba shi da tushe balle makama. Sanarwar ta ce “labarin jaridar intanet ta Sahara Reporters ta wallafa da ke zargin cewa ministan ya sayawa matansa uku gidajen a Abuja karya ne. Tun da ministan ya kama aiki a bai sayi gida ko daya ba, kuma gidan da yake zaune ciki ya kama shi ne tun a watan Janairun 2017, shekara biyu kenan gabanin ya kama aiki”. sanarwar ta kuma ce sauran gidaje biyun da jaridar ta wallafa ba ma a san daga inda ta samo su ba. Bugu da kari ta yi kira ga al’ummar kasar da su yi watsi da wannan kokarin bata wa Minista Ali Pantami suna da ake kokarin yi HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Ni Ba takardar dala bace da zaka kalmashe kasa a Aljihu – Godwin Obaseki

Ni Ba takardar dala bace da zaka kalmashe kasa a Aljihu wannan kalami bai yiwa magoya bayan Ganduje dadi ba Tu lokacin da aka nada Ganduje a matsayin shugaban komitin yakin neman zaben APC a jahar Edo magoya bayan Godwin Obaseki sukai ta yiwa Gwamna Ganduje martani, Kamar yanda wani dan PDP a jahar maisuna sunday idona ya bayyana cewa shugaban su Godwin Obaseki ba takardar dala bace da Ganduje zai saka acikin Aljihu Tabbas wadannan kalamai basu yiwa magoya bayan APC dadi ba musamman a jahar Edo, Idan baku manta ba wannan kwamiti de zaa rantsar dashi ne a ranar 6 ga wannan wata a babban birnin tarayya Abuja, Amma babban abun tambaya anan shine yaushe maganar dala zata kare? HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Akwai Yiwwuwar Messi Yabar Barcalona

Akwai Yiwwuwar Messi Yabar Barcalona Akwai yiwwuwar Leonel Messi ya bar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcalona ta duba da yadda dubunnan matsaloli suka kunno kai a ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Barcalona ahalin yanzu da gasar Laliga tazo ƙarshe. Hakan ya farune ganin yadda Messi yake zargin mai horas wa Setien akan shine ya jefa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcalona a yanayi mara daɗi ahalin yanzu musamman agasar Laliga duba da cewa kofin yana neman kubucewa ƙungiyar ta Barcalona Ayanzu dai ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta baiwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcalona tazarar maki huɗu inda wasanni biyarne suka rage a kammala gasar inda agobe Asabar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Villarreal zata kara da Barcalona. Messi dai ya bayyana cewar shifa yana ganin buga ƙwallonsa a Barcalona tazo ƙarshe inda take tunanin zai bar ƙungiyar a shekarar 2021 anan gaba kenan.   HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Gwamnan Bauchi ya dakatar da sarkin misau

Gwamnan Bauchi ya dakatar da sarkin misau sakamakon tashin hankula da ake samu a yankinsa Gwamnan jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya Bala Muhammad Kaura, ya dakatar da Sarkin Misau, Alhaji Ahmed Sulaiman sakamakon tashin hankali da aka samu a yankin tsakanin manoma da makiyaya. Tashin hankalin a wannan mako, a garin Zadawa da ke cikin karamar hukumar ta Misau, ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum tara da jikkata wasu da dama. Gwamna Bala Kaura ya sanar da dakatar da Sarkin ne yayin kaddamar da wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan rikici mai nasaba da wani fili da ake takaddama a kai. Gwamnan na jihar Bauchi ya kuma dakatar da wasu sarakunan gargajiya masu mukaman hakimi da dagaci a yankin da rikicin ya shafa. Sarkin Misau dai na daga cikin manyan sarakunan gargajiya a jihar ta Bauchi. Tun farko gwamnan ya dakatar da shugaban riko na karamar hukumar ta Misau da wasu manyan jami’an karamar hukumar. Gwamnatin jihar na zarginsu da yin sakaci game da rikicin. Gwamnan ya ce an dakatar da jami’an da sarakunan gargajiyar ne domin bayar da damar gudanar da bincike. Dakatarwar za ta ci gaba da aiki zuwa lokacin da za a kammala bincike. An ba kwamitin binciken da aka kaddamar makwanni uku ya gabatar da rahotonsa. Kawo yanzu ba a kai ga jin ta bakin shuwagabannin da aka dakatar ba. A 2015 ne dai aka nada Alhaji Ahmad Sulaiman Sarkin Misau, bayan rasuwar Sarki Muhammadu Manga. Ba a cika samun rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar ta Bauchi ba idan aka kwatanta da wasu jihohin Najeriya masu fama da irin wannan rikici da ma matsalar ‘yan bidiga. HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

zamuci zaben edo ko da inconclusive ne – Gwamna Ganduje

Zamuci zaben jahar edo ko da inconclusive ne jim kadan bayan nada Ganduje a matsayin shugaban yakin neman zaben gwamnan jahar edo. Jama’a dayawa basuyi mamakin nada gwamna Ganduje a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamna a jahar Edo ba. Musamman yanda ake ganin gwamnan a matsayin wanda ya samu nasara bayan cire tsammani da magoya bayansa sukai, Wani futaccen dan Gandujiyya Abdullahi Abubakr kiru ya bayyana cewa tunda aka nada Ganduje a matsayin shugaban yakin neman zaben osaze ize-iyamu, zasu ci zabe koda da inconclusive ne, Idan baku manta ba wannan kwamiti za a rantsar dashi ne a ranar 6 ga wannan wata damuke ciki a babbar sakatariyar APC a Birnin tarayya Abuja. Nadin Ganduje de a wannan matsayi yasa mutane dayawa a jahar kano zargin cewa dama uwar jam iyya ta kasa tana sane da yanda aka gudanar da zaben kano, Shiyasa ma suke kokarin nada Ganduje a matsayin shugaban yakin neman zaben gwamnan na edo, Lokaci de shine bamu damar sanin dalilin dayasa akai wa Gwamna Ganduje wannan babban mukami a Jam iyyar APC,   HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Jami’iyyar APC za ta iya darewa gida biyu – Bola Tinubu

Jam iftar APC zata iya darewa gida biyu bayan Rikicin gida data da baibaye jamiyyar inji bola Ahmad tinubu   Kasantuwar samun wadansu matsaloli a cikin jam’iyyar APC, inda har ta kai ga musayan yawu a tsakanin shugabannin Jam’iyyar, wanda hakan ya sa a halin yanzu tafiyar jam’iyyar za ta fara tafiya da murya biyu. Daga bisani mun samu rahoto inda Bola Tinubu yake ganawa da manema labarai a garin Legas, bayan sun tashi wani zama na gaggawa da wadansu ba’adin ‘kabilar Yarbawa, ciki har da wadansu ba’adin ‘kabilar Hausawa, don cimma matsayar tafiyar jam’iyyar ta APC a kashin nasu tunanin. Hakan ya ‘kara bude wani sabon fai-fai ne, inda Tinubu yake cewa sune suka yi fadi tashi don ganin an tabbatar da jam’iyyar ta APC, har ta samu karbuwa ga al’ummar Nijeriya’ babu kudanci babu Arewa, kuma farin jinin jam’iyyar APC ta shiga lungu da sako Amma duk da haka Tinubu ya yi wadansu kalamai, inda yake nuna alamun zai yi baya-baya da tafiyar ta APC a halin yanzu, nan da wadansu lokaci kadan, don yin nazari tare da wadansu jiga-jigan Jam’iyyar, inda za su fitar da matsayar su a tafiyar. Kana an samu karin wadansu bayanai inda Tinubu yake cewa dole su yi wa APC kwaskwarima, kodako babu tunanin wadansu masu fada aji a cikin jam’iyyar ta APC, kuma suna da tabbacin idan suka kawo wannan tunanin lallai za a iya samun sauyi na tafiyar ta su. HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

yan majalisa sun dakatar da Buhari Akan aikin, N-POWER

Yan majalisar tarayya sun dakatar da shugaba Buhari kan shirin daukar maaikata a tsarin N-power kimanin 774,000 Majalisun Tarayya a Najeriya sun dakatar da shirin gwamnatin ƙasar na ɗaukar ma’aikata masu ƙaramin ƙarfi 774,000 har sai sun samu cikakken bayani kan tsarin ɗaukar mutanen da za su ci gajiyar shirin. Matakin ya zo ne kwana guda bayan ƙaramin ministan kwadago Festus Keyamo ya yi zazzafar jayayya da ‘yan majalisar lokacin da suka nemi ya yi musu bayani yayin wani zama da suka yi ranar Talata. Haɗin gwiwar majalisar ƙwadagon ya buƙaci sanin hanyar da aka bi aka zaɓo ayarin mutum 20 daga kowacce jiha a Najeriya don yin aikin tantance mutanen da za a ɗauka aikin na wucin gadi Cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar, zaurukan majalisar sun bukaci kwamitocinsu na kwadago su gayyato babban ministan ayyuka na ƙasar Chris Ngige ba tare da ɓata lokaci ba. Shugaban kwamitin kwadago na majalisar wakilai Hon. Muhammad Ali Wudil ya shaida wa BBC cewa damuwarsu ita ce gwamnati ta bijiro da shirin ne don amfanin jama’ar da suke wakilta, don haka suke bibiya don ganin an yi adalci da tabbatar da daidaito. Dole mu bibiya mu tabbatar da yadda aka yi aka zaɓo ayarin mutum 20 da za su yi aikin ɗauko matasan da za su ci gajiyar shirin,” in ji ɗan majalisar. Ya ce sun nemi a dakatar da shirin ne saboda a matsayinsu na majalisa suna da haƙƙi a yi musu bayani don su tabbatar an yi daidaito. Ministan ya zargi ‘yan majalisar da ƙoƙarin karkatar da shirin da ofishinsa ya ɓullo da shi don cin moriyar masu ƙaramin ƙarfi. Wasu rahotanni ma sun ambato Festus Keyamo na cewa jayayyar ta taso ne saboda ‘yan majalisar sun buƙaci sai ya ba su ƙari a kan kashi 15% da ya ware musu tun da farko, abin da shi kuma ya ce ba za ta saɓu ba. Shi dai Muhammad Ali Wudil ya ce ministan ya shaida musu a yayin zaman ranar Talata cewa ‘yan majalisar ba su da ikon su tambaye shi game da yadda aka zaɓo mutanen da za su ɗauki ma’aikatan. Sun nemi kashi 15% a cikin duk mutum 1,000 da za a ba aiki Dan majalisar ya ce ba shi da wata masaniya kan zargin da ministan ya yi cewa sun nemi kashi 15% a cikin duk mutum 1,000 da za a duk ƙaramar hukumar Najeriya tsawon wata uku. “A matsayina na shugaban wannan kwamiti, wallahi tallahi ƙarye ne. Ni dai ta ɓangarena bai ba da wani alƙawarin kaso 15 ba. Kwata-kwata, ba ai haka ba,” cewar Ali Wudil. “Ba mu buƙata ba, shi kuma bai bayar ba.” Ya ƙara da cewa idan ma haka ne, a matsayinsu na wakilan ‘yan Najeriya suna da ‘yancin gabatar da koke-koken jama’arsu don ganin sun shiga cikin wannan shiri don a dama da su. Da aka tambayi Muhammad Ali Wudil ko me ya sa ba su yarda da buƙatar minista Festus Keyamo na ci gaba da zaman a gaban ‘yan

Continue reading

Ganduje yazama shugaban yakin neman zaben gwamnan Edo

Da dumi: An nada Ganduje shugaban kwamitin yakin zaben gwamnan jihar Edo na APC Kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) karkashin jagorancin gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ta nada kwamitin mutane 49 domin yakin neman zaben gwamnan jihar Edo. Za’a gudanar da zaben ne ranar 19 ga watan Satumba, 2020. Majiyar Legit ta samu labarin cewa an nada gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, matsayin shugaban kwamitin, yayinda gwamnan Imo, Hope Uzodinma, zai zama mataimakin kwamitin kuma Abbas Braimoh a matsayin sakatare. Mataimakin kakakin jam’iyyar ya bayyana cewa za’a rantsar da kwamitin ranar 6 ga Yuli, 2020 a sakatariyar jam’iyyar dake Abuja. Dan takaran jam’iyyar APC, Osaze Ize-Iyamu zai kara da na PDP, Godwin Obaseki, bayan dambarwan siyasan da ya gudana tsakaninsu.       HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading

Manchester City za ta dauko Grealish, Sannan Kuma Chelsea na zawarcin Gomes

Manchester City za ta dauko Grealish, Sannan Kuma Chelsea na zawarcin Gomes sannan kuma Manchester city zata duba yiwuwar dauko Jack grealish. Manchester City za ta duba yiwuwar dauko dan wasan Aston Villa Jack Grealish, mai shekara 24, idan Bayern Munich ta sayi dan wasan Jamus Leroy Sane, mai shekara 24. An ce ita ma Manchester United tana zawarcin dan wasan na Ingila. (Telegraph) A shirye Chelsea take ta dauko dan wasan Manchester United Angel Gomes. Kungiyoyin kasashen waje da dama suna zawarcin dan wasan na Ingila dan shekara 19. (Independent) Kazalika Manchester United tana son dauko Grealish domin maye gurbin Gomes. (Express) Newcastle da Arsenal suna cikin kungiyoyin Gasar Firimiya da ke son sayo dan wasan Wolfsburg dan kasar Netherlands Wout Weghorst, mai shekara 27, a kan euro 35m. (Bild – in German) Southampton na sha’awar sayen dan wasan tsakiyar Arsenal Folarin Balogun, dan shekara 18. (Mail) Haka kuma Southampton tana duba yiwuwar dauko dan wasan gaban Faransa Thomas Robert daga Montpellier. Matashin dan wasan mai shekara 19, da ne ga tsohon dan wasan Newcastle Laurent Robert. (Mail) Chelsea ta amince golan Kamaru Andre Onan, mai shekara 24, da dan wasan bayan Argentina Nicolas Tagliafico, mai shekara 27 su koma Ajax. (Sun) kamar yanda BBC ta ruwaito. Dan wasan da ke tsaron bayan Paris St-Germain Layvin Kurzawa ya sabunta kwangilar shekara hudu a kungiyar. An yi ta rade-radin cewa dan wasan na Faransa, mai shekara 27, zai koma Arsenal ko Liverpool. (Goal) Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce kungiyar wacce ta lashe Kofin Firimiya na bana ba za ta kashe “miliyoyin kudi” a kasuwar musayar ‘yan kwallon kafa. (Mirror) ‘Yan wasan Barcelona da dama suna zaman-tsama da kocin kungiyar Quique Setien. (ESPN) Dan wasan Leicester City Dennis Gyamfi, dan shekara 18, zai bar kungiyar idan kwangilarsa ta kare yau, 30 ga watan Yuni. Matashin dan wasan na Netherlands ya ki amsa tayi da dama da kungiyar ta yi masa na sanya hannu kan kwangila. (Leicester Mercury) Zaku iya ci gaba da kasancewa damu a wannan fage na wasanni tare da ni Aminu Asarab HausaTrustThe admin user of HausaTrust.com.

Continue reading