Aisha Tsamiya Itace tafu kowacce Jaruma Shigar Mutunci A shekarar 2019

Aisha Tsamiya Itace tafu kowacce Jaruma Shigar Mutunci A shekarar 2019 a buncien da jaridar Hausa Trust Tayi a karshen makonnan me karewa

 

HausaTrust logo

Duk wani me kallon fina finan Hausa ya kwana da sanin irin kalubalen dake cikin wannan masana anta musamman inda jamaa sukafi mai da hankali wajan shigar da jarumai mata keyi acikin fina finan hausa wanda jamaa suke ganin hakan bai kamata ba a tsarin Addinin musulunci,

amma a baya masu shirya fina finan suna kafa hujjane da cewar suna fadakar da masu irin wannan shigar banzane, domin baze yiwu ace yarinya zata futo a mutuniyar banza ba kuma a ganta ta saka hijab wannan dalilin shiyasa zaku ga mace tana shigar banza a film,

wasu dayawa sun karbi wannan uzuri nasu amma wasu kuma basu karba ba.

sai kuma gashi yanzu ba acikin film din bama zaka ga jaruma wacce sunan ta ya sanu a duniya tayi shigar da bata dace da koyar war addinin musulunci ba musamman ma idan zatayi bikin birthday.

idan baku manta ba ko a karshen wannan shekara futacciyar jarumar nan Rahama sadau tayi bikin birthday wanda tayi wata shiga ana ganin cinyarta inda malamai da dama suka hau kan wannan lamari suka dinga caccakar wannan jaruma,

sai kuma jarumar nan zainab indomi itama a shekarun baya wasu hotunanta sun zaga duniya wadanda suma sun tashi kura acikin wannan masana anta,

sannan a kwanakin baya ma akwai futacciyar jarumar nan Amina Amal itama data futar da wasu hotuna akai ta surutu a kansu duk da ita haryanzu ba a kara ganin ta saki irin wadannan hotunan ba,

sai kuma tsohuwar jarumar nan kubura dako itama an futar da wasu hotunan ta wadanda suka kewaye kafafen sada zumunta,

sai kuma futacciyar jarumarnan Hauwa waraka wacce itama wani hotonta ya dinga zagaye kafafen sada zumunta wanda akace shatin nonuwanta sun futo,

futacciyar jarumar nan Aisha Tsamiya itace kawai ta ciri tuta acikin wadannan jarumai wanda ba a taba kamata da irin wannan hotuna na shigar banza ba kuma duk wani maabocin kallon fina finan hausa yasan ko acikin film wannan jaruma baza ka ga tayi irin wannan shiga ta banza ba.

sai kuma jarumarnan maimuna wata yarinya itama de za a iya cewa bata irin wannan shigar banza, da kuma sauran wasu jarumai wadanda buncike bekai kansu ba,

 

HausaTrust logo

(Visited 2,958 times, 1 visits today)