Na tsani talaka kuma bazan taba iya auran sa ba - Jamila

Na tsani talaka kuma bazan taba iya auran sa ba – Jamila

Wata budurwa mesuna Jamila wacca ta ce ta tsani talaka kuma baza ta iya auran sa ba, ta yi mi’ara kuma baya inda take nuna cewa kawarta ce ta ci amanarta

A wannan satin ne wani hoton bidiyon wata budurwa me suna Jamila ya karade ko ina inda tayi furucin ta tsani talaka kuma bazata auri talaka ba. Sai gashi yanzu ta futo tana bawa jama’a hakuri akan wannan furuci da tayi.

Ta bayyana cewa kawarta ce me suna Halima Tasi’u ta yada bidiyon a duniya kowa ya gani. Amma sunyi wannan abun ne a wasa inda tace mata tagogeshi, tace to.

Bayan kwanaki sai suka sami matsala da ita kawar tata sai ita Halima taje gidan wata kawarsu mai suna Rabi ta tura mata. Ita kuma Rabi sai ta turawa mijinta mai suna Hamisu Mamman Reza. Shi kuma yana kasar Libiya, shine shi kuma ya dinga turawa mutane har ya yadu a duniya.

“Abisa wannan dalilinne wani saurayi na muna soyayya dashi akan ze aureni ganin wannan bidiyon yasa yace ya fasa aurena saboda haka dan Allah duk wanda ya ke da wannan bidiyon ya goge kuma Allah ya isa tsakanina da Halima,” inji Jamila.

(Visited 628 times, 2 visits today)