Tallan Rigar Nono Ya Saka Anayiwa Jaruma Maryam Booth Magan Ganun Batsa

Tallan Rigar Nono Ya Saka Anayiwa Jaruma Maryam Booth Magan Ganun Batsa a shafunta na instagram wasu suna ganin hakan bai dace ba

HausaTrust logo

Maryam Booth ta sha zagi a wajen masoyanta akan tallar rigar nono da tayi ashafunta na instagram Fitacciyar Jaruma Maryam Booth tasha tofin Allah tsine ga mabiyanta na shafin Instagram

Jarumar ta sha bakaken maganganun ne bayan ta wallafa wasu rigunan nono a shafinta inda take tallatasu akan kudi naira dubu goma sha shida babu ragin ko sisi

Mabiyanta da yawa sun zage ta akan wannan kaya da ta wallafa, inda wasu kuma suka dinga yi mata nasiha akan cewa hakan da ta yi bai kamata ba kuma bai dace ba amma wasu suna ganin hakan ba laifi bane musamman yan uwanta mata,

Jaruma Maryam Booth ta sha kalamai marasa kan gado na rashin da’a daga mabiyan shafinta na Instagram sakamakon tallata wasu samfurin rigunan mama da tayi a shafin ta akan zunzurutun kudi har naira dubu goma sha shida (N16,000), kowacce guda daya.
Jarumar dai ta wallafa hoton rigunan ne a shafinta inda ta kuma rubuta a kasa da harshen turanci cewa rigar nono La Senza ta sayarwa akwai lamba 36C da kuma 34D, farashinsu dubu goma sha shida duk guda daya.

Jim kadan da wallafa wadannan hajoji nata sai ta fara shan martani inda mafi akasarin masu korafin tsadar rigar nonon mata ne, inda wasu ke cewa rigar nonon 16,000 zasu siya kuma su dora mata wata rigar a saman ta, wata budurwa kuwa cewa tayi watakila ko tayi kuskure ne tana nufin dozen ne a wannan farashin.

Sai dai jarumar ta mayar da martani da cewa ita wannan rigar mama ta La Senza haka kudinta yake ga wanda ya san farashinta, kowa ya san me tsada ce, sannan kuma ga wanda yake tantama zai iya bincikawa a shafin La Senza na yanar gizo domin tabbatar da farashin na ta.

A bangaren samari ‘yan bana bakwai kuwa abin ya kazanta domin maganganu na rashin da’a suka dinga yiwa jarumar.

Wasu daga cikin mabiyan nata masu kaifin hankali sun fadakar da ita cewa a matsayinta na mace kuma sananniya bai kamata ta tallata irin wannan kayan sawar mata na ciki ba wanda mafi yawanci ansan mata da boye su zai fi kyau ta sai da su a shago ko rumfa inda matan za su je su siya amma ba ta wallafa a shafinta

HausaTrust logo

(Visited 2,992 times, 6 visits today)