Allah Yayiwa Shariff Rabiu Usman Baba Rasuwa Yau a Birnin Kano

Innalillahi wa inna ilaihirrajuun Allah yayiwa shariff Rabiu Usman Baba Rasuwa yau acikin birnin kano sakamakon gajeriyar rashin lafiya da yayi

HausaTrust logo

Rabi u usman baba futaccen mawakin manzon Allah ne wanda yayi shuhura a kano da ma najeriya baki daya ya rasu yau a kano bayan yasha fama da yar gajeriyar rashin lafiya, kuma zaayi janaizarsa ayau da misalin karfe uku na yamma a gidan sheikh isyaka rabiu, daganan kuma zaa kaishi makabartar kofar mazugal,

sharif Rabiu usman Baba ya dade yana wakar yabon manzon Allah SAW wanda zaka iya cewa duk wani me yabon manzon Allah a jahar kano to Rabiu Megidansa ne,

kuma idan baka mantaba shine wanda ya fara anfani da fiyano wajan yabon manzan Allah SAW inda lokacin haryayi wata waka mai suna Rabbi Rabbi wanda bayan futar da wannan waka sharif rabiu usman baba ya sha calanjin awajan wasu malaman jahar kano akan wannan waka,

wannan abu da ya faru har sai da sheikh dahiru usman bauchi ya shigo wannan magana kafun wannan kura ta lafa daganan ne fa masu majalisi suka samu damar yin wakokin su na zamani kamar yanda akeyi yanzu,

sharif Rabiu usman baba de ya tara muridai da yawa wanda hakan yasa baya samun damar sukunin rabuta wakoki da yawa  ba kamar yanda akasanshi a da ba,

Tabbas Rashin wannan babban masoyin manzon Allan a kano ba karamun rashi jahar tayi ba bama jaha ba za a iya cewa kasa baki daya da kuma manyan masu majalisi a jahar kano, muna rokon Allah yasa Annabi Ya karbi bakuncinsa

(Visited 6,280 times, 4 visits today)