Sarkin Kano Sunusi Na ll zai nada Naziru M Ahmad Sarkin Waka

Sarkin Kano Sunusi Na ll zai nada Naziru M Ahmad Sarkin Waka

Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na ll zai nada shahararren mawakinnnan Naziru M Ahmad Sarkin Waka na yankin arewacin Nijeriya.

Idan baku manta ba a kwanakin baya de Sarki Sunusi ya nada wani mawaki dan kudancin kasarnan sarautar waka inda jama’ar yankin arewa suke ganin cewa yakamata mai martaba sarki ya waiwayi wannan mawaki Naziru M Ahmad tunda tunkafun ya zama sarki Naziru yake masa waka.

Lokacin da aka nada Muhammadu Sunusi Dan Majen Kano, Naziru M. Ahmad yai masa wata futacciyar waka wacce takarade nahiyar Hausa. Sannan kuma bayan an nada shi Sarkin Kano ma Nazirun ya dada futo da wata futacciyar waka wacce itama ta karade nahiyar Hausa mai suna MATA KU DAU TURAME YAYI, KUMA KUCE NADI DAI ANYI, SARKIN KANO SUNUSI NA BIYU UBAN MATASA YAYI. Wannan wakar dama wasu wakoki da dama da Nazirun yayiwa Sarkin Kano Muhammadu Sunusi.

Wai shin kuna ganin wannan sarauta da za a yiwa Naziru M Ahmad ya caccanta kuwa?

(Visited 4,457 times, 1 visits today)