Ganduje Yasa Anyo Waje Da Kayan Ofis Din Sheikh Aminu Daurawa

wai mene dalilin da yasa gwamnatin Ganduje Tasa Akayo Waje da kayan sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Aka kuma gar kame ofis din nasa a jiya talata

HausaTrust logo

 

gwamnatin Jahar kano ta saka An rufe ofis din shugaban hukumar hisbah sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a jiya talata mun tuntubi shehin malamin yace shi bai ma san me akeyi ba sai yanzu yake jin labarin amma dama shi ya dau hutu domin ayanzu haka yana shirye shiryen zuwa umara

dama dai tun lokacin da daurawan yakaiwa jagoran darikar kwankwasiyya ziyarar nuna goyon baya ake ta jiran wannan rana sai kuma gashi kwatsam anjiyo bullar wannan al amari

majiyar Jaridar Hausa Trust ta jiyo cewa dama a halin yanzu zaman doya da manja akeyi a tsakanin daurawan da gwamnati tun lokacin da ya bayyana raayinsa akan bidiyon dala inda daurawan bai goyi bayan gwamnati ba yace kawai a tsaya ayi bincike a bawa mai gaskiya gaskiyar sa

Tun a wancan satinne dai aka gano sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a Gidan madugyun darikar kwankwasiyya tare da rakiyar wasu daliban sa dan nuna goyon baya ga jagoran darikar kwankwasiyyar,

HausaTrust logo

(Visited 974 times, 1 visits today)