Wai Shin Da Gaske Ne Anayin Lalata Da Mace Kafun Asakata a Film?

wai shin da gaskene ana yin lalata da mata yan film kafin asaka su a film, kalmar zina kalmace da a ka dade ana jifan yan film da ita mazansu da matansu

HausaTrust logo

masana antar kannywood tabbas masana anta ce wadda ta kunshi dubunnan matasa maza da kuma mata masu jini a jika da kuma dattijai suma maza da mata amma kasan cewar matasan sun nunka dattijai nesa ba kusa ba a masana antar shine musabbabin jifan wannan masana anta da muna nan kalamai,

A bangare daya kuma zaka iya cewa su kan su matasan masana antar maza da mata suna da laifi wanda dolene jamaar gari su jefesu da kalaman batanci saboda rashin kamun kai da suke dashi mazansu da matansu,

musanman ma idan kai laakari da hotunan da suke yawo a kafafen sada zumunta kamar facebook instagram da kuma twitter na yan film mazansu da matansu wani hoton idan ka gani bakaso kka kara kallonsa ba musanman ma mata

sannan ana zargin daraktoci da frodusas na cikin wannan masana anta da idan zasu saka mace a film sai sunyi lalata da ita kafun a sakata a film

amma wasu daga cikin manyan taurarin film da kuma daraktoci sun musanta wannan zargi, idan baku manta ba a kwanakin baya BBC tayi hira da  futacciyar jarumar nan Hauwa waraka da aka tambayeta akan wannan batu sai tace,

Nidai babu wanda ya taba zuwar mun da wannan bukatar na yayi lalata dani kuma ba wata mace da ta taba gayamun cewar wani namiji ya nemi yayi lalata da ita ba, sai dai kasan wannan harkar kowa da halinsa yazo babu wanda za ka bayar da shaida a kansa,

sannan jarumar ta kara da cewa  suma matan ai ba yara bane  ba bu yadda zaayi ace zaa kama mace da karfi ayi lalata da ita sai dai idan ita takai kanta,

futaccen jarumi Ali nuhu kuwa da aka tambayeshi akan wannan batu cewa yayi ni gaskiya ban taba samun wacce tace mun an nemi ayi lalata da ita kafun a sakata a film ba  kuma ina ganin wannan zargi ba gaskiya bane domin kuwa muna kokarin kare addininmu da al adarmu kuma akwai kwamiti dake sanya ido akan masu neman yin lalata da yan film da ma kula da yadda muke har kokin mu

shikuwa futaccen darakta Aminu saira cewa yayi wannan batu ba gaskiya bane hasali ma wannan ne karo na farko  da akayimun tambaya irin wannan,kuma ina ganin da ace ana samun irin wannan lalata da matan da suka gabata anji sunyi korafi, karka manta wasu daga cikin matannan sunyi aure da ace haka batun yake da idan wasu sunyi shiru wasu sai sunyi magana,

HausaTrust logo

(Visited 6,396 times, 10 visits today)