Shin Kasan Dalilin Dayasa Ali Nuhu Yacire Yarsa Fatima Daga Harkar Film ?

Shin meyasa Ali Nuhu ya cire yarsa Fatima daga harkar film, tambayar da yan jarida sukaiwa Ali nuhu kenan saboda an dade baa ganin fatima acikin film,

HausaTrust logo

Futaccen jarumin nan Ali nuhu wanda ya amsa sunan sarki a masana antar shirya fina finan hausa dake arewacin najeriya wato kanny wood .,saboda daukaka da kwarjini da Allah yabashi, gami da dogon zamani da ya kwararo yana sharafinsa, a masana antar, batare da an samu wani jarumi da ya sha gabansa ba,

 

kuma sannan ba wani zamani da akayi aka denajin duriyasa a masana antarba,zamu iya cewa tun bayyanar jarumin a karni na goma sha tara tauraruwar sa ke haskawa haryanzu,

mafi yawancin jaruman de da ake damawa dasu acikin wannan harka yaransa ne manya da kanan jaruman da suke cikin wannan masana anta ka iya cewa kusan wannan shine musabbabin da Ali Nuhu ya zama babban jagora akan duk wani jarumi har ma yake rike da wannan masana anta har ake masa lakabi da sarki,

tun daga kan Adam a Zango , Sadiq Ahmad Sadiq Sani Sadiq Zaharaddin Sani Lawal Ahmad manya kenan sai kuma kananan jarumai irinsu Garzali miko da Shamsu dan iya sai Ramadan Both, da de sauran su,

A mata kuma akwai irinsu Nafisa Abdullahi da Rahama Sadau da kuma Maryam Yahaya, sai wa yanda sukai aure irin su Rahama Hassan da Fati Ladan zamu iya cewa Ali nuhu ya fi kowanne jarumi futo da jarumai sababbin fuska har suyi suna,a harkar film,

zaka iya cewa Harkar fil de tayiwa jarumi Ali nuhu riga da wando kasan cewar sanadin harkar film ya samu makudan kudade da bashi da saa a masana antar idan ka dauke jarumi Sani Danja da kuma Marigayi Rabbilu Musa Ibro,

Kamar de yadda kuka sani jarumi Ali nuhu Allah ya azurtashi da yaya biyu mace da namiji Ahmad Ali nuhu da Kuma Fatima Ali nuhu, wanda tun suna kanana Ali nuhu ya cuso su cikin harkar film,

bayan wasu lokuta de an dena ganin fuskar fatima Ali Nuhu acikin film, sai namijin wato Ahmad wanda tauraruwarsa take haskawa acikin jaruami yara wanda har lambar gir mamawa aka bashi, wanda hakan ya jefa shakku a idanun masu kallo har suke jefa ayar tambay cewa meyasa aka dena ganin fuska fatima Ali nuhu acikin  film,

dama de wasu dayawa suna ganin rashin dacewar hakan na saka yarsa mace acikin wannan harka saboda wasu dayawa sunayiwa wannan harka ta film kallan matattara ta sharholiya

Jarumi Ali nuhu ya bayyanawa yan jarida awata hira da yayi a shekarar da ta wuce da gidan rediyon freedom inda ya amsa tambay kan batun dena ganin yarsa acikin fina finai inda yace shi bai cire yarsa daga harkar film ba, kawai dai ita fatiman ce bata shaawar futowa acikin fina finai kasan kowa da raayin sa, Ali nuhu ya kara da cewa ni nakan baiwa yayana dama su zabi abunda suke da shaawar yi,

 

to ahamad yana da shaawar yin film shiyasa ake ganinsa acikin fina finai itakuma fatima tafu shaawar bangaren dinki wato fasion and disigned shiyasa aka dena ganinta wannan shine dalili ba wani abu ba,

HausaTrust logo

(Visited 11,445 times, 28 visits today)