Atiku zai kwashe kwanaki biyu kacal a AMURKA

Atiku zai iya bawa Buhari matsala a kasar amurka kuwa? ganin yanda da jamiyya me mulki tai ta ikirarin Atiku bazai iya zuwa amurka ba,

 

HausaTrust logo

dan za’a tuna an dade ana yamadidin cewar Atiku ba zai iya taka kafarsa ya shiga kasar Amurka ba sakamakon nemansa da suke yi ruwa a jallo da nufin kamashi biyo bayan zarge zargen rashawa dake rataye a wuyansa dakuma matarsa Jamila

Karshen tika tika tik! kowa yasan yan da ja iyya me ci tadunga kunfar baki cewa Atiku be isa yaje amurka ba , sai kuma gashi kwatsam dan takarar shugaban kasar a inuwar jam’iyyar adawa ta PDP , watau Alhaji Atiku Abubakar ya taka kafarsa a kasar Amurka a ranar Alhamis 17 ga watan Janairu, Atikun ya isa kasar Amurka, tare da daraktan yakin neman zabensa, shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki,

inda ma suka sauka a otal din shugaban kasar Amurka, Trump Hotels. wanda akwanakin baya yan majalisar amurka suka sanyawa titin da wannan hotel din yake sunan barack obama,

Wannan ziyara ta Atiku ta tayar da kura a farfajiyar siyasar Najeriya, musamman ta yadda yan Najeriya da dama suna da tabbacin tabbas idan Atiku ya shiga Amurka sai Amurka ta kamashi, don haka magoya bayansa ke musu dariya a yanzu, kuma martabarsa ta karu a idonsu.Sai dai jami’I mai magana da yawun Atiku Abubakar, Paul Ibeh ya bayyana cewa iya kwanaki biyu kacal Atiku zai kwashe a kasar Amurka tare da tawagarsa,

kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.Haka zalika sanarwar ta kara da cewa Atiku zai gana da yan kasuwar Najeriya dake zama a kasar Amurka, zai kuma yi gemu da gemu da jami’an gwamnatin kasar Amurka, da kuma kungiyar yan Najeriya mazauna kasar Amurka. amma da alama wannan ziyara zata iya kawowa shugaba buhari cikas,

(Visited 168 times, 1 visits today)