Miji Da Mata film ne me Dogon zango wanda zaku fara kallo ranar 1 ga watan October

Miji Da Mata film ne me Dogon zango wanda zaku fara kallo ranar 1 ga watan October

Duk wanda yake bibiyar harkokin fina finan hausa yasan cewa ayanzu haka kasuwar film din takoma YouTube

Kusan hakan ne dalilin dayasa masu shirya fina finan suka koma shirya fina finai masu Dogon zango wanda akafi sani da series

Kamfanin brothers point multimedia ya shirya wani kayataccen film na barkwanci wanda zai fara sakinsa a YouTube ranar 1 ga watan October

A tashoshin YouTube kamar haka brothers tv entertainment murnatv kundin nishadi da hausatrust sai kuma hausa series tv

Tabbas film din zai nishadantar kwarai dagaske kasancewar manyan jarumai da akasa aciki musamman dan wasan barkwancinnan Suleiman Bosho

An hakikance cewar film din zai iya samun karbuwa kasancewarsa ya tabo Abubuwan da suke Faruwa acikin gidajenmu musamman kan kishi

Ali Bet de shine ya shirya wannan film sannan malam Aminu Asarab yabada umarnin sa

 

(Visited 95 times, 4 visits today)