shin kunsan dinbun masoyan da suka tarbi tsohon sarki sunusi a Kaduna?

Tsohon sarki sunusi ya samu tarbar masoya masu dunbun yawa a ciki da wajan jahar Kaduna

Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ziyarci gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai.

Wannan ce dai ziyara ta farko da sarkin ya kai wata jiha ta Najeriya tun bayan da ya tare a Legas bayan cire shi daga sarauta a watan Maris.

A wani saƙo da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce Sarki Sanusi ya yi alƙwarin yin iya bakin ƙoƙarinsa a matsayinsa na shugaban Jami’ar Kaduna, da kuma mataimakin shugaban hukumar bunƙasa zuba jari ta jihar.

Kwanaki kaɗan ne bayan cire sarkin daga sarauta gwamna El-Rufai ya ba Sarkin waɗannan muƙaman

 

(Visited 106 times, 3 visits today)