Afakallahu zai dauki matakin dakatar da saka film me Dogon zango a jahar kano

Shugaban Hukumar tace fina finai a jahar kano Ismail na Abba Afakallahu zai dauki matakin saka film me Dogon zango a jahar kano,

Kamar yadda kuka sani dai zaa iya cewa harkokin film din hausa ayanzu kusan kaso sittin acikin dari zamu iya cewa sun koma kan YouTube kuma yawancin masu saka film a YouTube suna sakashi ne ba tare da Hukumar tace fina finai sun taceshi ba,

Kuma yawancin yan downloading suna kwafar wannan film a YouTube su dinga siyarwa da mutane batare da sun siya ba

Kusan hakanne yasaka wannan Hukumar daukar wannan mataki amma wasu dayawa daga cikin masu shirya wadannan fina finai sun amunce da wannan mataki na wannan hukuma,

A tattaunawar da mukai da shugaban kungiyar masu YouTube na arewa Ali Bet kuma shugaban kamfanin brothers tv entertainment ya bayyana mana cewar

Munji dadin wannan mataki da wannan hukuma zata dauka sakamakon mutane suna futa su kashe kudinsu suyi wadannan fina finai kudadensu basa dawowa kawai de sunayine domin su ruke tasharsu amma sai ake samun wasu daga cikin masu downloading suna kwafar wannan film suna sayarwa da mutane batare da sun saya ba amma idan wannan hukuma tashigo to zaa samu wani tsari wanda masu shirya fina finai masu Dogon zango zasu dunga samun kudin shiga

Ali bet ya bayyana mana cewa ayanzu kanfaninsa yana shirye shiryen daukan wani film me Dogon zango mai suna MIJI DA MATA wanda yace idan har wannan hukuma ta dauki wannan mataki to hakan zai dinga basu damar kawo fina finai masu kayatarwa

A yanzu de zamu iya cewa ana daf da cimma matsaya tsakanin Hukumar tace fina finai da kuma masu YouTube a jahar kano

(Visited 163 times, 1 visits today)