Akwai Yiwwuwar Messi Yabar Barcalona

Akwai Yiwwuwar Messi Yabar Barcalona

Akwai yiwwuwar Leonel Messi ya bar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcalona ta duba da yadda dubunnan matsaloli suka kunno kai a ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Barcalona ahalin yanzu da gasar Laliga tazo ƙarshe.

Hakan ya farune ganin yadda Messi yake zargin mai horas wa Setien akan shine ya jefa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcalona a yanayi mara daɗi ahalin yanzu musamman agasar Laliga duba da cewa kofin yana neman kubucewa ƙungiyar ta Barcalona

Ayanzu dai ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta baiwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcalona tazarar maki huɗu inda wasanni biyarne suka rage a kammala gasar inda agobe Asabar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Villarreal zata kara da Barcalona.

Messi dai ya bayyana cewar shifa yana ganin buga ƙwallonsa a Barcalona tazo ƙarshe inda take tunanin zai bar ƙungiyar a shekarar 2021 anan gaba kenan.

 

(Visited 43 times, 1 visits today)