zamuci zaben edo ko da inconclusive ne – Gwamna Ganduje

Zamuci zaben jahar edo ko da inconclusive ne jim kadan bayan nada Ganduje a matsayin shugaban yakin neman zaben gwamnan jahar edo.

Jama’a dayawa basuyi mamakin nada gwamna Ganduje a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamna a jahar Edo ba. Musamman yanda ake ganin gwamnan a matsayin wanda ya samu nasara bayan cire tsammani da magoya bayansa sukai,

Wani futaccen dan Gandujiyya Abdullahi Abubakr kiru ya bayyana cewa tunda aka nada Ganduje a matsayin shugaban yakin neman zaben osaze ize-iyamu, zasu ci zabe koda da inconclusive ne,

Idan baku manta ba wannan kwamiti za a rantsar dashi ne a ranar 6 ga wannan wata damuke ciki a babbar sakatariyar APC a Birnin tarayya Abuja.

Nadin Ganduje de a wannan matsayi yasa mutane dayawa a jahar kano zargin cewa dama uwar jam iyya ta kasa tana sane da yanda aka gudanar da zaben kano,

Shiyasa ma suke kokarin nada Ganduje a matsayin shugaban yakin neman zaben gwamnan na edo,

Lokaci de shine bamu damar sanin dalilin dayasa akai wa Gwamna Ganduje wannan babban mukami a Jam iyyar APC,

 

(Visited 984 times, 1 visits today)