Manchester City za ta dauko Grealish, Sannan Kuma Chelsea na zawarcin Gomes

Manchester City za ta dauko Grealish, Sannan Kuma Chelsea na zawarcin Gomes sannan kuma Manchester city zata duba yiwuwar dauko Jack grealish.

Manchester City za ta duba yiwuwar dauko dan wasan Aston Villa Jack Grealish, mai shekara 24, idan Bayern Munich ta sayi dan wasan Jamus Leroy Sane, mai shekara 24. An ce ita ma Manchester United tana zawarcin dan wasan na Ingila. (Telegraph)

A shirye Chelsea take ta dauko dan wasan Manchester United Angel Gomes. Kungiyoyin kasashen waje da dama suna zawarcin dan wasan na Ingila dan shekara 19. (Independent)

Kazalika Manchester United tana son dauko Grealish domin maye gurbin Gomes. (Express)

Newcastle da Arsenal suna cikin kungiyoyin Gasar Firimiya da ke son sayo dan wasan Wolfsburg dan kasar Netherlands Wout Weghorst, mai shekara 27, a kan euro 35m. (Bild – in German)

Southampton na sha’awar sayen dan wasan tsakiyar Arsenal Folarin Balogun, dan shekara 18. (Mail)

Haka kuma Southampton tana duba yiwuwar dauko dan wasan gaban Faransa Thomas Robert daga Montpellier. Matashin dan wasan mai shekara 19, da ne ga tsohon dan wasan Newcastle Laurent Robert. (Mail)

Chelsea ta amince golan Kamaru Andre Onan, mai shekara 24, da dan wasan bayan Argentina Nicolas Tagliafico, mai shekara 27 su koma Ajax. (Sun) kamar yanda BBC ta ruwaito.

Dan wasan da ke tsaron bayan Paris St-Germain Layvin Kurzawa ya sabunta kwangilar shekara hudu a kungiyar. An yi ta rade-radin cewa dan wasan na Faransa, mai shekara 27, zai koma Arsenal ko Liverpool. (Goal)

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce kungiyar wacce ta lashe Kofin Firimiya na bana ba za ta kashe “miliyoyin kudi” a kasuwar musayar ‘yan kwallon kafa. (Mirror)

‘Yan wasan Barcelona da dama suna zaman-tsama da kocin kungiyar Quique Setien. (ESPN)

Dan wasan Leicester City Dennis Gyamfi, dan shekara 18, zai bar kungiyar idan kwangilarsa ta kare yau, 30 ga watan Yuni. Matashin dan wasan na Netherlands ya ki amsa tayi da dama da kungiyar ta yi masa na sanya hannu kan kwangila. (Leicester Mercury)

Zaku iya ci gaba da kasancewa damu a wannan fage na wasanni tare da ni Aminu Asarab

(Visited 23 times, 1 visits today)