‘yan sanda zasu biya ‘yan shi’a kimanin miliyan 15 a matsayin diyya

‘yan sanda zasu biya ‘yan shi’a kimanin miliyan 15 a matsayin diyya bayan zargin da sukai na an kashe musu mutane 3 kuma an hanasu gawar waki.

Wata babbar kotun tarayya a Abuja, ta umarci ‘yan sandan Najeriya su biya ‘yan kungiyar Shi’a mabiya Shaikh Ibrahim Elzakzaky Naira miliyan 15 saboda kisan ‘ya’yan kungiyar uku yayin wata zanga-zanga a Abuja.

Kotun wacce ta yi zamanta a Abuja babban birnin kasar ta kuma umarci babban asibitin kasa ya bayar da gawarwakin uku nan take domin yi musu jana’iza.

A ranar 22 ga watan Yulin 2019 ne aka kashe wasu mabiya kungiyar ta Shi’a yayin wata zanga-zanga da ta rikide zuwa tarzoma.

Alokacin zanga-zangar su ma ‘yan sanda sun yi zargin cewa ‘yan Shi’a sun kashe dan sanda, zargin da kungiyar ta IMN ta musanta.

Lauyan kungiyar ta IMN Bala Isa Daku ya ce sun garzaya kotun ne bayan hukumomi sun ki ba da gawawwakin domin yi musu jana’iza Kamar yanda Addini ya tanadar.

A hukuncin kotun karkashin mai shari’a Taiwo Taiwo, ya ce ‘yan sanda za su biya Naira miliyan ga kowanne mamaci a matsayin diyyar kisan da aka yi.

Sai dai kotun ta yi watsi da bukatar cewa a tilasta wa ‘yan sanda su nemi afuwar kisan.

Kamar yanda kuka sani de har yanzu shugaban kungiyar yan uwa musulmi ta shi’a wato sheikh Ibrahim El zakzaky de yana hann.

Kusan zaa iya cewa ruke wannan babban malami shine dalilin dayasa mabiyansa ke yawan yin zanga zangar.

 

(Visited 23 times, 1 visits today)