Innalillahi wa inna ilaihirrajuun || Ansamu Yawai Mata Masu Cikin Shege Bayan Rufe Makarantu

Innalillahi wa inna ilaihirrajuun Ansamu yawaitar matan da suke samun cikin shege bayan rufe makarantu, sabida bullar korona,

Jami’ai a Kenya sun ce ana samun karuwar ‘yan matan da ke yin ‘cikin shege’ a kasar, musamman tun bayan sanya matakan takaita zirga-zirga sakamakon barkewar annobar cutar korona a watan Maris.kamar yanda BBC ta ruwaito,

Wasu bayanai da ma’aikatar lafiya ta saki sun nuna cewa a yanki daya kawai an samu ‘yan mata dubu hudu da suka yi ciki tun farkon shiga shekarar nan.

An rufe makarantu a fadin kasar a tsakiyar watan Maris a wani bangare na daukar matakan kariya da gwamnati ta yi.

Hukumomin sun nuna damuwa cewa a mafi yawan lokuta dangin ‘yan matan ne ake samu da hannu a lamarin.

Jami’ai sun kuma nuna fargabar cewa yawan na iya fin haka saboda ba a faye bayar da rahotanni kan cikin ‘yan mata ba.

Shugabannin siyasa a yankunan Kenya 47 sun nemi gwamnati da ta yi bincike kan karuwar adadin.

Kenya ce take da mafi yawan ‘yan matan da ke yin ciki a duniya, inda ake samun haihuwa 82 daga cikin 1,000.

(Visited 106 times, 1 visits today)