zanga zangar da akeyi a arewacin Najeriya zai iya bata aikin da sojoji keyi inji Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zanga-zangar da ake yi don nuna adawa da kashe-kashen da ke faruwa a arewacin Najeriya na iya ɓata ayyukan da sojoji ke yi a yankin.

A wata sanarwa da fadar gwamnatin kasar ta fitar a ranar Talata mai dauke da sa hannun mai taimaka wa Shugaba Buhari kan yada labarai Malam Garba Shehu, shugaban ya yi kira ga al’ummar jihar Katsina da kar su fitar da rai kan sojoji wadanda ake da yakini a kansu shekaru da dama da suka wuce na yadda suke shawo kan rikice-rikice. Kamar yanda jaridar BBC ta ruwaito,

Sanarwar ta kuma bai wa ‘yan kasar tabbacin cewa dakarun sojinta za su iya magance matsalar fashi da makami da ta’addanci, inda ta ce a kara hakuri ana daukar matakan da suka dace na kare rayukan ‘yan kasar.

Hakan na zuwa ne bayan da a ranar Talatar da safe wasu kungiyoyi da dama suka fatsama kan tituna a birnin Katsina da ke arewacin Najeriyar inda suka yi kira a dauki mataki game da kashe-kashen da ke faruwa a yankin.

Masu zanga-zangar, mai taken #ArewaIsBleeding a Turance, wato ‘Jini yana kwarara a Arewa’, sun bayyana matukar bacin ransu kan halin ko-in-kula da suke zargi gwamnatocin kasar na yi kan yawaitar kashe-kashe a yankin.

Sun ce za su gudanar da irin wannan zanga-zanga a jihohi 19 da ke arewacin kasar don matsa lamba ga gwamnati ta dauki matakin da ya dace kan masu kashe-kashen.

Sanarwar ta ce Shugaba Buhari – wanda ya bayar da umarnin samar da wata tawaga ta musamman ta ‘yan sanda da sojoji don magance rashin tsaro a jihohin Naija da Katsina da Sokoto da Zamfara, ya ba da tabbacin cewa za a kara sa ido, ta hanyar yin shawagi da jiragen sama da daddare, wadanda tuni aka samar da su karkashin shirin arangamar da sojoji ke yi a yankin mai taken “Operation Accord”.

An kaddamar da wannan runduna ta arangamar ne mako uku da suka gabata.

”Sojojin Najeriya sun nuna za su iya a baya kuma za su sake tabbatar da cewa a wannan karon ma za su iya shawo kan matsalolin da ake fuskanta,” in ji shugaban kasar a cewar sanarwar.

Shugaba Buhari ya kuma bai wa al’ummar jihar Katsina hakuri da neman su bayar da goyon baya ga ayyukan soji da ke faruwa a jihar.

A karshe ya mika sakon jajensa da ta’aziyya ga wadanda suka rasa masoyansu.

”An gano manyan dazuzzuka a arewa maso yammacin kasar inda ya zama yankin da ‘yan fashi da makami ke buya. Sojoji za su lalata wadannan dazuzzuka,” a cewar shugaban.

Rahotanni sun nuna cewa makon da ya gabata kadai ‘yan bindiga da mayakan Boko Haram sun kashe mutum fiye da 100 a hare-haren da suka kai jihohin Katsina da Borno.

Gwamnatin kasar ta sha cewa jami’an tsaro suna magance matsalar tana mai cewa galibin hare-haren da ake kai wa na gyauron ‘yan bindiga ne, ko da yake ‘yan kasar na cewa hakan ba gaskiya ba ne.

Ranar Litinin kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce gwamnatin Najeriya ta gaza kare rayukan ‘yan kasar yayin da matsalar tsaro take ci gaba da yin kamari musamman a arewacin kasar. Kamar yanda shafin BBC Hausa ya bayyana.

 

 

(Visited 92 times, 1 visits today)