Shin yakamata ayi koyi da matan film kuwa? amma sai gashi ance ayi koyi da tsamiya

AishaAliyu Tsamiya ita kadaice macen da yakamata yan mata suyi koyi da ita musamman ta bangaran saka sutura, a Binciken da jaridar hausatrust ta dada yi,

Aisha Aliyu tsamiya ita kadaice tafuta zakka acikin dukkanin matan da suke cikiin masana’antar hausa film, kuma ita kadaice yakamata yan mata da matan Aure suyi koyi da ita Musamman a bangaran saka kayan mutunci,

Idan kuna bibiyar harkokin fina finan hausa tabbas akwai mata sama da hamsin wadan da jarumai ne acikin wannan masana anta, kowacce idan ka dauko ta sai kaga bazaka iya cewa ayi koyi da ita ba musamman awajan saka kayan mutunci,

Aisha tsamiya tabbas ta ciri tuta ko acikin film bazaka ganta ta saka kayan da zasu futar da surar ta ba, zamu iya cewa idan ka tara mutum dari masu kallan film ba lalle ka samu wanda ya taba ganinta da kananan kaya ba,

Tabbas yakamata matan film suyi koyi da Aisha tsamiya idan har sun yarda suna koyar da tarbiyya ne,

(Visited 83 times, 1 visits today)