tsohon sarki sunusi yace Najeriya tana shirin fadawa bashin da bazata iya biya ba

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce Najeriya tana shirin fadawa bashin da ba za ta iya biya ba idan ta ci gaba da tafiya da irin salon shugabancinta

 

Kamar yadda The Punch ta bayyana, Sanusi ya sanar da hakan ne a wani shiri da Emmanuel Chapel ya jagoranta mai taken ‘hanyar shafe illar COVID-19 ga tattalin arziki da kuma hanyar farfadowa’.

Ba tun yanzu ba Sanusi yake Kira ga gwamnatin tarayya ba ta rage yawan kudin data ke kashewa don hakan ba zai haidar da da mai ido ba. Kuma ba zai kawo daidaituwar battalion arziki ba,

Yace kamata yayi gwamnati ta sake yawan hanyoyin samun kudade ta hanyar kara maaikata a fannonin kwon lafiya da ilimi

Sarkin ya kara da cewa yana da tabbacin cewa raguwar kudin shiga a bangarorin man fetur zai iya sawa lila sai munci bashi Dan biyan maaikata albashinsu.tsohon sarki yace dolene a duba

Acikin kundin tsarin mulkin dolene mu samu shugaban kasa, da mataimakinsa dolane mu samu minister daga kowacce jaha

Dolane my samu shugabanni kana nan hukumomi 774 a fadain kasarnan kuma tilas ne su samu masu bada shawara da kuma mataimaka daban daban

Daga wannan kiyasin mun shirya cin bashin da bazamu iya biya ba

Ina ta maganar nan na tsawon shekaru a wannan tsarin da muke bi zamu samu daidaito kuwa zuwa wani lokaci?

Tsohon sarki yace wannan tattaunawar yakamata mu dinga yi,

 

(Visited 285 times, 1 visits today)