Rarara ya gwangwaje mawakin kwankwasiyya da dankareriyar mota da kudi Naira miliyan 1

Futaccen mawaki rarara ya gwangwaje mawakin kwankwasiyya da sabuwar mota da kudi limamin miliyan daya,

A ranar Juma’a, 12 ga watan Yuni 2020, Fitaccen Mawakin Siyasar Nahiyar Afrika Dauda Kahutu Rarara ya gwangwanje Mawaki Aminu Lawal Dumbulun da Dalleliyar mota kirar kamfanin Peugeot ( Peugeot Continue of Discussion) da kuma kudi kimanin Naira Miliyan daya.

Rarara ya yi wa Dumbulun wadannan kyaututtuka sakamakon ficewa da ya yi a siyasar Kwankwasiyya ya dawo Gandujiyya a cikin watan da ya gabata.

Dumbulun dai yana a cikin sahun gaba na Mawakan Kwankwasiyya wanda ya rika yin wakoki barkatai a lokacin yakin neman zaben Kwankwaso, ya kuma yi wasu wakokin na jinjina ga tsohon Gwamnan Kano, Eng. Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso.

Tun a ranar 30 ga watan Mayu, 2020 mawakin ya bayyana ficewar sa a tafiyar Kwankwasiyya, inda ya bayyana cewa ya dawo tafiyar Gwandujiyya saboda irin yadda ya yaba da halin mawaaki Rarara da kuma dattakon sa na kishin mawaka ‘yan uwan sa.

Tuni dai Dumbulun har ya yi sabuwar waka mai taken ‘Ku gayawa Makafi Ku bude Ido akwai Rijiya’ wadda a cikin ta yake yabon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, tare da yin shagube ga mabiya Kwankwasiyya.

Fitattun wakokin da Dumbulun ya yi a lokacin da yana Kwankwasiyya sun hada da, Tashi Barci Kasa, Ga Zaki Ma Ci Abokan Gaba, Rugum Da Rugum Sai Tsawa, Mu Makafi Ne Bamu Ganin Kowa.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da Mabiya Kwankwasiyya suka fara yin mubaya’a a sanadiyyar Dauda Kahutu Rarara ba.

(Visited 84 times, 1 visits today)