shugaban kasa Buhari zai kashewa kano wasu makudan kudade,

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da izinin biyan dala miliyan 318, kimanin aira biliyan 123 domin fara aikin titin jirgin kasa daga Legas zuwa Kano.

Za a biya kudin ne a matsayin kason Najeriya na 15 cikin 100 na aikin titin jirgin wanda zai ci dala biliyan 5.2 a hadin gwiwar Najeriya da Kasar China.

Da yake sanar da hakan, Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya ce ana sa ran fara aikin titin jirgin kasan kafin karshen watan Agusta kamar yanda jaridar Aminiya ta ruwaito,

“Muna sa ran da zarar an kammala tattaunawa da kamfanin CECCC na kasar China za a fara aikin a karshen watan Agusta ko Satumba”, inji minister Amaechi.

Ministan wanda ya ce gwamnatin China na taimakawa kuma ta riga ta bayar da kasonta na dala biliyan 1.6 na shekarar 2020.

Gwamantin China ta taimaka sosai. Ta riga ta ba da dala biliyan 1.6 na titin jirgin. Muna fata kafin watan Oktoba za ta ba wa Najeriya rancen na dala biliyan 5.3 domin fara aikin kamar yanda jaridar Aminiya ta ruwaito,

A hirarsa da gidan talbijin na Channels a daren Juma’a Amaechi ya ce Majalisar Zartaswa ta kasa ta yanke shawarar tattara ribar da aka samu daga sufurin da za a yi ta titin jirgin domin biyan bashin da za a karba a gina shi.

Da yake fatan samun riba da zarar titin jirgin ya fara aiki musamman idan aka fara dakon kaya, Amaechi ya ce a yanzu layin jirgin Abuja-Kano da a baya ke tara naira miliyan 46 a wata ba, na tara naira miliyan 109 zuwa miliyan 110 a wata.

Ya kara da cewa ana fatan gama biyan kudin aikin kafin ma a kammala aikin, domin samun daman fara aikin titin jirgin kasa da zai tashi daga Fatakwal zuwa Maiduguri.

Muna rokon Allah ya tabbatar da wannan aiki

(Visited 49 times, 1 visits today)