Gwamnatin Jahar Kano Zata Rufe Wasu Kasuwanni A Jahar Dan Gudun Yaduwar COVID 19

Gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Ganduje ta ce za ta rufe wasu daga cikin kasuwannin da ke jihar tare da tsananta dokar hana shige da fice a kan iyakokinta

HausaTrust logo

Hakan kuwa ya faru ne sakamakon bullar muguwar cutar coronavirus a jihar a ranar Asabar dinnan data gabata,
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya shaidawa BBC cewa tuni aka killace wanda aka samu da cutar a asibitin Pfizer na kwanar Dawaki.
Dan shekaru 75 din da haihuwa na nan a killace don hana yaduwar cutar a jihar. Ganduje ya ce, ya zama dole gwamnatin jihar ta dauki matakai masu tsanani don hana cinkoson jama’a duk da hakan zai iya takura al’ummar jahar
A halin yanzu, jihar Kano ta zama cikin jihohin Arewa da aka samu bullar muguwar cutar tun bayan bullar cutar a jihohin Kaduna da Katsina hakan nema yasa jiya aka sanya dokar hana futa a garin daura
Wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa ya bayyana cewa mutumin da ke dauke da cutar coronavirus a jihar Kano ya je sallar Juma’a a Masallaci. Wannan lamarin kuwa ya jawo rudani da tsananin tashin hankali ga manyan jami’an gwamnatin jihar.
Idan zamu tuna, jihar Kano din ta samu mutum na farko mai dauke da cutar ne a ranar Asabar, 11 ga watan Afirilu. An gano cewa an kwantar da mutumin ne a wani asibiti mai zaman kansa da ke GRA Nasarawa a jihar Kano.
Wata majiya daga asibitin ta bayyana cewa an kwashe dukkan ma’aikata da majinyatan asibitin inda aka killacesu. An gano cewa, an kara da kwashe wasu masu makwabtaka da asibitin don gwaji,
Majinyacin dai yana da shekaru 75 kuma tsohon jakada ne. Ya isa Kano ne daga Legas, inda ake zargin ya debo cutar. Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa, kanwarsa da aka aika an hana ta shiga gidan iyalan mutumin.
Hadiman gidan tare da iyalansa da ke kwatas din Giginyu duk an kwashe su zuwa cibiyar killacewa. Hankalin jama’a mazauna wurin ya matukar tashi bayan gano cewa mutumin na dauke da cutar.

HausaTrust logo

(Visited 366 times, 1 visits today)