Jahar Kano Zata Iya Zarce Ko Wacce Jaha a Yawan Mutanan Da Suka Kamu Da COVID-19

jahar kano zata iya zarce duk wata jaha a yawan mutannan da suka kamu da wannan cuta ta covid 19 sakamakon ziyartar manyan gurare uku da me cutar yayi

HausaTrust logo

mutumin da ake zargi ya kamu da cutar corona a jahar kano ya ziyarci wasu manyan gurare guda uku wanda ake zargin hakan ka iya jawowa dubban jamaa ka iya kamuwa da wannan cuta,

tabbas idan hakan ya tabbata jahar kano zata iya zarce duk wata jaha a yawan masu dauke da wannan cuta,

mutumin ya ziyarci masallacin jumaa a wannan jumaar data gabata wanda yai muamala da mutane da dama a wannan masallaci wanda tabbas hakan ya jefa jamaar jahar kanocikin rudani

sannan mutumin ya ziyarci wani asibutin kudi dake cikin jahar kano wanda anan ma yayi muamala da mutane da dama a wannan asibiti,

sannan ya ziyarci wani katon quaters inda gidansa yake nan ma yayi muamala da mutane dayawa wanda tabbas hakan shima mutane dayawa sun shiga rudani,

jahar kano de ta samu wannan cuta a karan farko ta hanyar wani mutum da akace yakai shekaru 70

kuma sannan angano cewar an kwantar da mutumin a wani asibitin kudi dake nasarawa GRA a jihar kanon, wata majiya daga asibitin ta bayyana mana cewa an kwashe dukkan maaikata da masu jinya na asibitin an killacesu,

wani mazaunin yankin ya bayyana cewa kanwarsa da aka aika an hana ta shiga gidan iyalan mutumin

sannan kuma hadiman gidan tare da iyalansa dake kwatas din giginyu duk an kwashesu zuwa cibiyar killacewa,

HausaTrust logo

(Visited 2,077 times, 1 visits today)