Bayan Naziru Ya Ajiye Rawaninsa Ana Hasashen Rarara Ko Alan Waka Zasu Iya Rabauta Da Wannan Rawani

Bayan Naziru Ya Ajiye Rawaninsa Ana Hasashen Rarara Ko Alan Waka Zasu Iya Rabauta Da Wannan Rawani na sarkin waka Nan bada jimawa ba

HausaTrust logo
HausaTrust

Idan baku manta ba a yau ne aka wayi gari da wata takarda wacce take dauke da sa hannun naziru m Ahmad wacce take nuna cewar ya sauka daga mukamin da sarki murabus wato muhammadu sunusi na biyu ya bashi

A sabida hakane jamaa dayawa suke ta zargin cewa wannan rawani za a iya damkashi ga Futaccenmawakin siyasar na wato Rarara ko kuma dan gaba gaba a masarutar wato Aminu Alan Wak’

Amma mutane dayawa suna ganin cewa babu ta yadda zaayi ma Alan ya rabauta da wannan rawani kasancewarsa dan jam iyyar Adawa kuma gashi kusan za a iya cewa shine na gaba gaba acikin mawakan da suke cikin wannan masarauta,

Amma bamu sani ba ko Alan zai iya dawowa gindin gwamnati domin rabauta da wannan rawani idan kwa ya gaza yin hakan to tabbas babu wanda zaa bawa wannan rawani idan ba futaccen mawakin siyasar nan Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara ba,

A irin tataburzar dake faruwa a jihar Kano sanadiyyar tsige tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, har ya zuwa yanzu dai lamarin yaki lafawa
Yayin da wasu ke murna da samun dami a kala, wasu kuwa sun koma gefe ne takaici ya dame su, duka sanadiyyar tsige Sarkin da gwamnatin jihar Kano tayi a ‘yan kwanakin da suka gabata.
Wata takarda da muka samu tana ta faman karakaina a shafukan sadarwa na zamani ta bayyana yadda Nazir Ahmad Sarkin Wakar San Kano ya ajiye mukaminsa da tsohon Sarki Sanusi ya bashi.
Takardar wacce aka rubuta ta a ranar 13 ga watan Maris dinnan tayi bayani kamar haka:
“Bismillahir Rahamanir Rahim!
“Na rubuta wannan takarda domin na sanar da hukuncin dana yanke na yin murabus daga mukamina na ‘Sarkin Wakar San Kano’, wanda zai fara daga yau 13 ga watan Maris na shekarar 2020. Ina godiya matuka akan wannan mukami da aka bani ba wai iya ga masarautar Kano ba, ina godiya ga jihar baki daya.
“Haka kuma, ina godiya ga masarautar da irin damar da ta bani na yin aiki da ita tsawon shekara daya da wani abu, wannan wata dama ce dana samu da kuma zan cigaba da cin ribarta har karshen rayuwata Ina fatan zaku yi na’am da wannan hukunci da godiya tawa.
Na ku a koda yaushe,
“Alhaji Nazir Muhammad Ahmad
to muna jira de muga wane zai rabauta da wannan rawani cikin wannan mawaka guda biyu

HausaTrust logo

(Visited 212 times, 1 visits today)