Ana Zargin Wani Malamin Makaranta Da Coronavirus a Katsina

Ana Zargin Wani Malamin Makaranta Da Coronavirus a Katsina jim kadan bayan dawowarsa daga kasar malaysia sannan an killaceshi waje guda

HausaTrust logo

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa babban sakataren ma’aikatar lafiya a jihar Katsina , Dakta Kabir Mustapha ya ce ana zargin wani mutum da coronavirus a jihar Katsina.

Haka kuma jaridar ta ce mutumin na killace a halin yanzu.

Kakakin Kungiyar Likitoci ta jihar, Dakta Yahaya Sodangi ya bayyana wa BBC cewa mutumin malami ne a jami’ar Dutsinma ta jihar katsina, FUDMA, da ya dawo daga kasar Malaysia kwanan nan.

Dakta Yahaya ya ce an dauki samfurin jinin mutumin don yin gwaji kuma ana sa rai sakamakon gwajin zai fito a yau Laraba,

sannnan kuma idan baku manta ba dama Hukumar yaki da yaduwar cutuka a Najeriya ta tabbatar da karuwar mutum 5 masu dauke da cutar coronavirus a kasarnan,

Hukumar ta ce duka masu dauke da cutar suna dawo ne daga Burtaniya ko Amurka kwanan nan.

Ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su kwnatar da hanklainsu yayin da jami’an kiwon lafiya ke daukar dukkan matakan da suka dace don yaki da yaduwar cutar a kasar.

Kawo yanzu mutum 8 ne aka tabbatar suna dauke da cutar a Najeriya.

kuma dama idan baku manta ba a dazu dazunnan najeriya ta hana baki shigowa daga China da Italy da Amurka da Birtaniya da Iran da Italiya da Korea ta Kudu da Sufaniya da faransa da Jamus da ma wasu kasashen da coronavirus ta yi kamari.

Hukumar hana kare yaduwar cututtuka ta kasar ce ta sanar da hakan a ranar Laraba a shafinta Twitter.

Sauran kasashen da Najeriyar ta hana baki shiga cikinta sun hada Koriya Ta Kudu da Spaniya da Faransa da Jamus da Norway da Netherlands da kuma Switzerland.

NCDC ta ce akwai masu dauke da cutar fiye da 1,000 a kowacce daga cikin kasashen nan.

Haka kuma, Hukumar ta sanar da cewa za a killace duka matifiya da za su iso kasar daga wadannan kasashen.

Sannan Najeriya za ta dakatar da ba da takardun shiga wato biza ga ‘yan kasashen nan 13

fatanmu Allah ka kawo mana karshen wannnan cuta a duniya baki daya,

HausaTrust logo

(Visited 154 times, 1 visits today)