Zargin Kashe Aure Da ake yiwa Hamisu Bureka Yana neman Zama Gaskiya/ Sadiya Haruna Tayi wani Dogon Bayani

Zargin Kashe Aure Da ake yiwa Hamisu Bureka Yana neman Zama Gaskiya/ Sadiya Haruna Tayi wani Dogon Bayani akan wannan balahira data auku

A hirar da wakilin jaridar hausatrust dake lagos yayi da sayyada sadiya Haruna kuma makusanciya ga Adam fasaha ta tabbatar wa da jaridar hausatrust cewar zargine ya kashe auran momi gombe da futaccen mawakinnan Adam fasaha,

Idan baku manta ba a safiyar jiya laraba ne kannywood exclusive suka saki wata tattaunawa da sukayi da momi gombe ta wayar tarho, inda momi take cewa ita haryanzu batasan dalilan dayasa Adam fasaha ya saketa ba bayan kwanaki 37 da Auransu inda ake zargin cewa futaccen mawaki Hamisu Breka shine ya kashe mata wannan Aure,
wakilin hausatrust ya tambayi sayyada sadiya haruna kasancewar ita makusan ciyar Adam fasaha ce tunda munyi kokarin muji ta bakin sa a kano amma abun yaci tura shin me ta sani game da lamarin Auran momi Gombe da Adam Fasaha sai ta ka da baki tace,
E abunda zance akan lamarin gaskiya shi Adam fasaha ba mutun ne me magana ba maganar gaskiya kenan ni a sanin da nai mishi kuma na tabbatar da cewa mutane sun masa wannan shaidar shide wannan auran da sukayi shekara daya daya wuce Allah ya jarabceshianyi aure an rabu kowane ma yana aure ya rabu da mace ba Adam fasaha kadai ba amma nayi mamaki ace shekara daya daya wuce da faruwar wannan abu amma suna tayar da maganar ban san dalili ba kuma abunda zance shide adamu tunda yayi hakuri ya bar maganar suyi hakuri suma su barta kada su tayar masa da tsohon ciwo,
sai muka tanbayeta ciwon so kenan take nufi kome sai tace.
aa ba ciwon so ba maana yanzu kamar ni mace ce akwai wata kawata datai aure ba auran soyayya bane aure kamar aka tilasta ta tayi Allah da iko yasa sati biyu kawai sukai wannan auran ya mutu duk da cewa batasan wannna mijin kuma anyi sati biyu ne aka rabu amma duk lokacin da aka gaya mata maganar abun na damun ta sabida sunyi zama koda na kwana daya ne to abunda nake nufi kenan,
to amma akwai zargin da ake tayi na cewar futaccen mawa kinnnan hamisu breka shine ya kashe musu aure da ita momi gombe shin kina da wannan labari sai sayyada tace mana
kwarai kuwa ina da wannan labarin amma tun ita momi gombe tana gidan shi Adamun sabida muna magana da Adamu yake cemun da bakinsa ita momi tana waya da Hamisu sannan kuma ita momin akwai lokacin da Adamu yana studio kamar yanda kukasan ofis dinsa a kano yaje aiki to be sani ba ashe momin tafuta taje suna case a folis tashon yana mijinta be kamata ma tafuta harma suna babban kes a steshon to bayan komawar sa gida sai yazo yace meyasa ba ai masa girki ba sai ta fara yi masa kame kame bata da lafiya daga karshe de har maganar tazo ta futa, sannan tana gidan Adamun tana waya da shi hamisun yanda shi ya gayamun kenan
kina nufun da hamisu breka suke kes din a folis teshon kowa? sai sayyada tace mana
a a bada hamisu bane da wani saurayi ne daban shima wani kes dinne wannan daban
to kenan akwai wata alaka da ita da hamisu bureka kenan ? nanma sayyada ta kada baki tace mana
E sosai kuwa akwai alaka sabida shi Adamun yana gaya mun kafun ya aure ta ita momi tsohuwar budurwar Hamisu Bureka ce sun taba soyayya a baya sun rabu shine abunda nake fada maka anan ai kasan duniya kuma kasan halinmu na hausa fulani ita tsohuwar budurwarsa ce ka gane koda tafuta a gidan auranta koda bashi da wani hannuaciki koma mene ne shi namijine kuma yana kasan hausa yasan me zaa fada kamata yayi ya dan ja jiki da ita sai ya kawota kusa dashi,
a yanda adamun yake ban labari ma kwanaki sunje abuja har cewa yake mushi irin sun hadu a Abuja  cewa yake hello Adamu gamunan fa mun futa da momi zamu dawo kagan be kamata ba cin fuska ne.
kamar yanda shi Adamun yake fadamun ,
to amma wannan magan ganun da kikeyi bakya ganin tunda yanzu duniya tana zarginki cewa ayanzu dake da Adamu fasaha kuna soyayya bakya ganin mutane zasuyi zargin cewar kishine yaja ki kike wannan magana sai sayyada ta ce mana,
to ai ni duk wanda yasanni kuma yana bibiyata idan Gaskiya tazo ko akaina ne zan fada
sai mukace mata wannan magana gaskiyace kenan
sai tace gaskiya ce amma bantabbatar ba amma abunda naji a bakin aminina shi nake fada shi Adamu fasaha kenan
mun tambayi sadiya haruna cewar akwai muryar ita momi gombe da kannywood exclusive suka saki in da take cewa da ita da iyayanta har yanzu basu san dalilin dayasa Adamu ya sake ta ba  shin kin san wannan maganar?
nasan da wannan maganan kuma naji hirar idan baka manta ba kafun mu fara maganar nan nagaya maka Adamu yace mun tana gidansa suna waya da shi bureka Adamu yacemun tana gidansa zata futa batare da ya sani ba tana gidansa suna babban kes a steshon batare da yasani ba to ai dole ma ya sakeki zargi acikin aure haramun ne in takaice maka zargi acikin aure ma babu aure mijinka yana zarginka kam ba gwamma auren babu ba
akwai auren da zakaga anayinsa aure sunna ce ta Annabi Muhammadu S.A.W bautane zaayine sabida kasamu Aljanna a karkashin mijinka amma wani auren  Allah na tuba kayafeni  sabon da ake gwamma babu wani auren zakai auran sabida ka samu lada ne amma a karshe sai a fada halaka gwamma babu sabida shi yana zarginta da abubuwan data keyi kuma a matsayinki na mace zakije nan danan zakije wani wajen dole ki gaya mijinki
amma har aje steshon a wuni ana kes mijinki bai sani ba ai wannna kadai ma ya isa ya bashi dalili na sakinki ko bai gayamun dalili ba amma irin wadannan abubuwan inaga shi yaja mata bata aje hankalinta a guri daya ba ko irin suna kallo da Adamu a falo haka idan tana kallon wakokin hamisu bureka kamar yanda Adamu yake gaya mun sai tace kai nasan da banyi aure ba dani zaayi to kaga gaba daya irin wadannan abubuwan tayi aurenne amma hankalinta yana waje
sai muka kara tambayar sayyada to kennan maganar da take cewa batasan dalilin dayasa Adamun ya sake ta ba kawai ta rufene kenan sai tace mana
Eh kwarai kuwa ta rufene kawai watakila kuma batasan tana aikata kasan a wasu lokutan ba wanda ya isa yace shi dede yakeyi a rayuwarsa gaba daya ba dole ana samun kuskure
kasan idan kana zama da mutanan kirki idan kana abu mara kyau zasu gaya maka amman kuma ida baka tare da mutanan da zasu fada maka kai kana yin abune mara kyau ne amma kai baka sani ba wata kila wannan futan data keyi aje steshon da sauran abubuwan data keyi idan bata tanayi ba to yau yakamata tasan tanayi kuma babu kyau idan ma bata sani ba kenan ina fatan ka fahimceni
to ance shi hamisu bureka aminin shi Adam Fasahane shin hakane ?
kwarai kuwa aminan juna ne na gaskiya da gaskiya
mun kara tanbayarta to ammma akwai wani na hannun daman hamisu bureka wato Ayatullahi tage wanda yai hira da tashar tsakar gida yace kusan wannan abu da aka taso dashi kawai anyine dan anemi suna shin me zaki iya cewa akan wannan maganar,
 Eh to da farko de kasan harkar industry kowa najin haushin kowa babu wanda yakeson kowa kuma abune na normal ko a ofis ne ko a aiki ne wanda kuka hada sanaa daya kasan akwai wannan kishin ita hassada ba karya bane kowa yana dashi sai dai na wani yafi na wani
maganar Ayatullahi tage daya keyi akan Adamu fasaha ai gwamma Adamu fasaha na farko alokacin da idan bazaku manta ba muna wani kes dinmu da wani wanda mukai auran mutu a dashi, Ayatullahi tagen har comedy yayi mun yana habaici yake cewa meyasa za a bawa yar iskar yarinyar nan kasida har da kiran sunan malam hafizu Abdallah toshi abunda yayi dunnan me zaa kirashi  shima sunan yake so yayi amma kuma ban bashi wannan popularity ba wayene bayaso yayi suna kowa yanaso yayi suna kuma kowa yanaso yagan shi wani ne
amma shi Adamu fasaha bashi ya tada futunan nan ba kuma tunda ake abunnan banji yayi magana ba tayaya zaace wai yanayi ne don yayi suna
ma ana kenan zargin da su bangaren su hamisu bureka sukeyi  ba haka bane kenan?
wallahi ba haka bane shide Adamu baikai kansa inda Allah bai kaishi ba kuma Alhamdulillah sana an dayakeyi ta waka tana masa rana saboda ayau Adamu zaka ganshi yaje biki waje kaza yaje biki waje kaza ai ba sai mutum yana postin a bubuwa a instagram bane ko kuma yana da folowas bane shi shine Adamu mutun ne shiru shiru kuma mutane sun sanshi da sana arshi kuma Adamu ba mai habaici bane kuma baya shiga lamuran mutane to su masu shiga lamuran mutane da habaice habaice ma mutane ba abunda bazasu fada ba komi kayi sai suce hassada
to amma da gaske sayyada sadiya haruna tana soyayya da Adamu fasaha ?
kwarai kuwa nace maka muna alaka dashi shekara takwas daya wuce wannan alakar daya hadani dashi ai soyayyace kuma har nazo nai aure sannan muka rabu da adamu kuma Allah yasa Auren be dade ba shekara biyu da wata uku nayi sai na futo to sai muka fara zumunci hakade ina nan lagos shi yana kano muna zumunchi in naje kano zanje har wajansa kuma muna chatin a waya sai yasa zumuncin mu bai kare ba,

(Visited 1,998 times, 18 visits today)